Ya saci akuya a barikin ’yan sanda

Alkalin Kotun, Maruff Mudashiru ya ba da belin wanda ake zargin a kan Naira dubu 200.

Ya saci akuya a barikin ’yan sanda

Akuya

Wani mai suna Chukwudi Ugwu ya gurfana a gaban wata kotun majistare a Ibadan Jihar Oyo bisa zarginsa da satar akuya a wani barikin ’yan sanda.

Mai gabatar da kara DSP Adewale Amos ya shaida wa kotun cewa wanda ake kara da wasu da suka gudu sun shiga Barikin ’Yan sanda na Iyaganku, Ibadan suka sace akuyar da kudinta ya kai Naira dubu 250 mallakar Olawole Oke.

Kuma ya zarge su da sace babur kirar Bajaj da ta kai Naira dubu 250 ta wani mai suna Dabid Adepoju, wanda hakan ya saba wa sassa na 516 da 390 (9) na dokokin manyan laifuffuka na Jihar Oyo.

Alkalin Kotun, Maruff Mudashiru ya ba da belin wanda ake zargin a kan Naira dubu 200 tare da dage shari’ar zuwa ranar 11 ga Yuli mai zuwa. (NAN)