Ya saci keke a harabar kotu
Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge ’Yan Alluna a birnin Kano ta tura wani matashi mai kimanin shekara 21 gidan maza don jiran shari’a bayan an gurfanar da shi gaban kotun bisa zargin satar keke a harabar kotun.Mutumin mai suna Usman Ibrahim wanda ya fito daga Jega a Jihar Kebbi ana tuhumarsa da satar keken hawa […]
Kotun Shari’ar Musulunci ta Fagge ’Yan Alluna a birnin Kano ta tura wani matashi mai kimanin shekara 21 gidan maza don jiran shari’a bayan an gurfanar da shi gaban kotun bisa zargin satar keke a harabar kotun.
Mutumin mai suna Usman Ibrahim wanda ya fito daga Jega a Jihar Kebbi ana tuhumarsa da satar keken hawa mallakar Rabi’u Abdullahi na Unguwar Birged a Kano yayin da aka ajiye keken a harabar kotun.
dan sanda mai gabatar da kara Shehu Adamu ya shaida wa kotu cewa mai keken ne da kansa ya yi nasarar cafke Usman a daidai lokacin da yake kokarin gudu da shi, kuma hakan ya saba wa sashi na 133 na Final Kod na shekarar 2000.
Da alkalin kotun Ma’ shari’a Abdu Abdullahi Waiya ya juya ga wanda ake zargin ya amsa laifinsa da ake zarginsa, don haka sai ya bayar da umarnin tsare shi a gidan maza zuwa ranar 25 ga Maris inda za a ci gaba da shari’ar.
A wani labarin kuma Kotun Shari’ar Musulunci da ke Fagge ta umarci wani fusataccen mai neman aure ya biya wani abokin nemansa diyyar Naira miliyan 17 da dubu 600, sakamakon cire masa ido da ya yi.
An gurfanar da Ibrahim Nasir mazaunin Kawo a karamar Hukumar Nassarawa bisa laifin cire idon abokin nemansa Muhammad Auwal na Unguwar Hotoro.
dan sanda mai gabatar da kara Shehu Adamu ya shaida wa kotun cewa Muhamamd Auwal ya kai kuka ofishinsu cewa abokin neman aurensa ya doke shi a ido lokacin da suka yi rigima a kan budurwarsu lamarin da ya sa idonsa ya samu rauni a karshe aka kai ga cire masa idon.
Da aka waiwaye wanda ake zargin ya amsa laifinsa, inda dan sanda mai gabatar da kara ya ce laifin ya saba wa sashi na 159 na kundin Final Kod.
Da yake yanke hukunci Alkalin kotun Mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya ya daure mai laifin shekara daya ko ya biya tarar Naira dubu 20. Sannan ya umarce shi ya biya diyyar Naira miliyan 17 da dubu 600 saboda lalata idon Muhammad Awwal, kuma ya biya shi Naira dubu 31 kudin maganin da ya kashe.