Ya sakale maciji a jikin kofar gidan ’yan haya
Irin macijin da wuya ya yi cizo, kuma idan ya yi cizon, ba ya da dafin da zai yi wa mutum lahani.
Wani mai gidan haya da ya fusata ya bullo da wata dabara ta nuna fushinsa ta hanyar sanya maciji a daidai wajen kulle kofar gidan, don ya nuna wa ’yan hayar cewa sun saba alkawari kan biyan kudin hayarsu.
Rahotanni sun ce, lamarin ya faru ne a garin Kitui na kasar Kenya, kuma hakan ya fara bayyana ne bayan da Gwamnan Jihar Nairobi, Mike Sonko ya wallafa hoton kofar gidan sagale da macijin a shafin Facebook.
- Mutum miliyan 46 ke bahaya a bainar jama’a a Najeriya — UNICEF
- Atiku ya taya Davido murnar zagayowar ranar haihuwarsa
A cikin hoton, ana iya ganin wani koren maciji a nannade a jikin wurin bude kofar mai launin kasa.
Da yake wallafa sakonsa kan batun, Sonko ya bayyana cewa, mai gidan hayar ya yanke shawarar sagale macijin a jikin inda ake bude kofar, kuma ya aikata haka ne saboda, “Masu hayar sun gaza biyan basussukan kudin hayar watan Satumba da Oktoba.”
Wannan rahoto da Sonko ya wallafa ya samu kusan martanin dubu 10, da kuma masu yin sharhi sama da 1,400 a shafin Facebook.
Sai dai an samu rabuwar kai kan goyon baya da sukar abin da mai gidan hayar ya aikata.
Wani mai suna Mwalimu Edwn Anton ya ce, sagale maciji a jikin kofar bai da wani amfani, saboda zai yi wuya irin macijin ya cutar da mutum don an gwada shi.
“Irin macijin da wuya ya yi cizo, kuma idan ya yi cizon, ba ya da dafin da zai yi wa mutum lahani,” kamar yadda ya rubuta.
“Ku ciro shi a jefar da shi kawai,” inji wadansu, yayin da Humble Boyie, ya ce sanya hoton “Rashin hankali ne.”
Timothy Mwetu ya ce, hoton “farfaganda ce da aka yi wa kwaskwarima, an tsara hakan ne don bata sunan Kenya.”
Kafar labarai ta Naija News ta ce sunan mai gidan Samuel Kioko, wanda yake zaune a yankin Kunda Kindu da ke yankin Kitui.
Kafar labarai ta Newsweek ce ta tuntubi Sonko da Ngeno da majalisar birnin Nairobi, don yin sharhi kan lamarin.