Ya saki matarsa don ta auri tsohon masoyinta bayan aurensu da shekara bakwai

Sai dai ba a bayyana cewa ko mijin ya rubuta wa matar takardar saki ba kafin ta auri masoyinta.

Ya saki matarsa don ta auri tsohon masoyinta bayan aurensu da shekara bakwai

Wani mutumin kasar Indiya ya ba jama’a mamaki bayan da ya saki matarsa da ya aura sama da shekara bakwai don ta auri wani masoyinta da suka yi shekaru suna soyayya kafin ta yi aure.

Mutumin mai suna Uttam Mandal da matarsa Sapna Kumari suna zaune ne a yankin Bhagalpur a Jihar Bihar a kasar Indiya.

Sun yi aure ne a shekarar 2014, inda suka haifi ’ya’ya biyu, kuma suna zaman aure cikin farin ciki da annashuwa.

Sapna ta yi soyayya da wani dan uwanta matashi mai suna Raju Kumar, kuma bayan ta yi aure yakan je kusa da gidan mijin a lokuta dabandaban.

Daga bisani mijin Sapna ya fahimci abin da ke faruwa da matarsa, hakan ya sa suka fara samun sabani.

Kuma bayan mijin Sapna ya  yi kokarin fahimtar da ita illar haka, amma sai abin ya ci tura, daga nan ne ya yanke shawarar taimaka wa matar tasa wajen biyan bukatarta ta auren wanda take matukar so.

An taba bayar da irin wannan labari a cikin shirin fina-finan Bollywood na kasar Indiya a cikin fim din “Hum Dil De Chuke Sanam,” wanda aka yi a 1999, kuma fim din ya shahara sosai inda jaruma Aishwaria Ray ta taimaka wa mijintaSalman Khan ya auri wata masoyiyarsa.

Ba kowa ba ne zai yi tunanin haka zai iya faruwa a rayuwa, hakan ne kuma ya bai wa wadansu mamaki, amma Uttam Mandal ya yi kokarin tabbatar wa jama’a abin da ya aikata a zahiri ya fi shirin fim.

“Na yi fushi da bakin ciki, amma zuwa wani lokaci sai na samu maganin abin da ke damuna,” Uttam Mandal ya bayyana wa kafar labarai ta ETB Bharat.

“Da ba a samu hanyar magance matsalar ba, da yanzu rayuwar mutum uku ta tagayyara a dalilin rashin neman fita.

Hakan ne kawai maganin matsalar. Yanzu dukkanmu kowa zai zauna cikin annashuwa da farin ciki,” inji shi.

A shekarun baya iyayen Sapna da surukanta sun yi ta yi ta mata nasiha kan ta zauna da mijinta Uttam kada ta bari aurensu ya kare, amma hakan bai yiwu ba.

Daga bisani mijin Sapna ya gayyaci iyaye da danginsu wajen bikin auren matarsa da masoyinta mai suna Raju Kumar.

Uttam Mandal ne ya shirya liyafar bikin auren tsohuwar matar tasa a wajen bauta na Durga da ke yankin Sutanganj a Jihar Bihar a Indiya.

A yayin bikin ya albarkaci auren da cewa, wannan hadin aure na har abada ne.

Ba a bayyana cewa ko Uttam ya rubuta takardar sakin Sapna ba, kafin ta auri masoyinta, amma a cewar kafafen labarai na Indiya ’ya’ya biyu da suka haifa suna tare da Uttam saboda Sapna ba ta amince ta tafi da su gidan sabon mijinta ba.

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya

Kano: Kwamishinan da Abba ya tsige ya koma Jam’iyyarAPC