Ya saki matarsa tana kan gadon asibiti saboda mele
Wata mata mai suna Asma’u Adamu da aka fi sani da Sabuwa da ke kauyen Lele a karamar Hukuma Soba a Jihar Kaduna, ta koka kan yadda mijinta ya sake ta a lokacin da take kwance a gadon asibiti saboda mele sakamakon konewar da ta yi lokacin da take yi musu girki.Asma’u wadda ta shafe […]
Wata mata mai suna Asma’u Adamu da aka fi sani da Sabuwa da ke kauyen Lele a karamar Hukuma Soba a Jihar Kaduna, ta koka kan yadda mijinta ya sake ta a lokacin da take kwance a gadon asibiti saboda mele sakamakon konewar da ta yi lokacin da take yi musu girki.
Asma’u wadda ta shafe shekara 14 tare da mijinta mai suna Adamu, ta bayyana wa Aminiya cewa ta kone ne kimanin shekara biyu a lokacin da take girka abincin buda baki a gidanta na aure. “Na dauki azumi na biyu shekaru biyu da suka gabata da misalin karfe 2:00 na rana na kammala jajjagen kayan miya na dauka da hanzari na shiga dakin girki sai na taka kwallon mangoro santsi ya kwashe ni na fadi a kan shinkafar da ke kan murhu tukunyar ta fallatso min a fuskata na fadi kwance. To akwai wata ’yar makwabtanmu ta zo sayen manja da ta ji shiru sai ta leko da ta ga halin da nake ciki sai ta ruga a guje ta kira jama’a aka zo aka fara ceton rayuwata,” inji ta.
Asma’u ta ce sai da kwashe mako biyu idanuwanta na rufe, kuma ta kwashe wata daya ana yi mata magani a gida ba tare da kai ta asibiti ba, sai daga baya ne aka kai ta Asibitin Koyarwa ta Jami’ar Ahmadu Bello da ke Shika inda aka karbe ta da kyar.
Ta ce, “Duk da halin da nake ciki kullum mijina Adamu na cikin zuciyata. Ina matukar kaunarsa, amma shi yana da wata manufa, wadda ya aiwatar a yayin da nake jinya a gadon asibiti.”
Asma’u ta ce sun kashe Naira dubu 130 a aiki da aka yi mata na farko, kuma ana cikin haka ne “Sai kawai mijina bayan ya ziyarce ni a gadon asibiti ya ce Asma’u, yanzu fa mutanen gari suna ta zagina cewa wai na bar iyayenki da hidimar asibiti saboda haka ina ganin gara na sake ki saki daya, idan Allah Ya yi kin fito daga asibiti kuma Ya nufi mu ci gaba da zaman aure ma ci gaba, amma yanzu ga takardarki. Nan take sai na fashe da kuka cikina ya kulle, mummunan bakin ciki ya turnuke ni. Da zan sauka daga hawa uku na asibitin in fito na samu fiya-fiya na saya na sha don na mutu na huta da wannan bakin cikin, sai Allah Ya hane ni na daure, Allah Ya sa min natsuwa na koma na zauna, na buga wa yayana waya na ce ya zo, bayan ya zo sai na mika masa takardar na ce Adamu ya sake ni, hawaye ya kara fito min. Sai yayana, ya fara lallashina tare da yi min nasiha, washegari iyayena suka zo suka kara lallashina suka ba ni hakuri.Sai na ce don Allah kada su je kwashe kayana da rana domin kada jama’a su san halin da ake ciki tunda har yanzu ba na son abin da zai cutar da mijina.”
Ta ce bayan komawarsu gida sai ’yan uwansa suka ziyarce ta suka ce me ya faru sun ga ana kwashe kayanta, ta fada musu suka ce wallahi ba wanda ya sani suka kara yi mata nasiha, suka kawo kudi suka ba ta.
Ta ce suna zaman lafiya da shi kansa mai gidanta da suka haifi ‘y’ya shida biyu suka mutu, haka da sauran’yan uwansa baki daya da amaryarta, kuma saboda zaman lafiyar da suke da kishiyarta idan maigidansu ya yi tafiya a dakinta suke kwana tare.
Duk kokarin da Aminiya ta yi a kauyen don ganawa da Malam Adamu, ya ci tura sai dai daya daga cikin wakilan Adamu, ya ce shi abin da ya sa ya sake ta shi ne ya ji iyayen matarsa Sabuwa da mutanen gari suna zarginsa da ba ya kula da ita kuma dawainiyar asibiti iyayenta ke yi, don haka ya sake ta. Ya ce a lokacin da ya yi sakin bai yi shawara da kowa ba, kawai ji suka yi cewa ya sake ta, kuma yanzu haka Adamu yana cikin damuwa.
Mahaifin Asam’u ya shaida wa wakilinmu cewa wannan al’amari ne daga Allah kuma duk abin da Allah Ya hukunta zai samu bawa sai ya same shi, don haka suna yi wa Allah godiya kuma suna rokon Ya ba su halin da za su dauki nauyin jinyarta a asibiti.