…ya samar wa masu noman kaji ribar biliyan 50 cikin wata 4
Masana’antar noman kaji ta kasa a yanzu tana da hannun jarin da ya kai kimanin Naira tiriliyan 1.6, sa’annan ya yi ajiyar kimanin Naira biliyan 50 a matsayin ribar da ya samu tun bayan rufe iyakokin kasar nan daga ranar 20 ga watan Augustan shekarar 2019. Shugaban Hukumar Kimiyar Dabbobi ta Kasa, Farfesa Eustace A. […]
Masana’antar noman kaji ta kasa a yanzu tana da hannun jarin da ya kai kimanin Naira tiriliyan 1.6, sa’annan ya yi ajiyar kimanin Naira biliyan 50 a matsayin ribar da ya samu tun bayan rufe iyakokin kasar nan daga ranar 20 ga watan Augustan shekarar 2019.
Shugaban Hukumar Kimiyar Dabbobi ta Kasa, Farfesa Eustace A. Iyayi ne ya sanar da haka a lokacin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja. Ya ce al’ummar Najeriya na cin kimanin miliyan 2 na tan ddn naman kaji a kowace shekara, yayin da ake kuma shigo tare da fasa kwaurin kashi 70 ta boyayyiyar hanya zuwa kasar nan; inda ya kara da cewa ba shakka rufe iyakar ya jawo wa masu harkar kaji na cikin gida aikin yi da ciniki.
Farfesa Iyayi ya ce idan wannan tan miliyan daya na kajin da ake hana shigo wa da su kasar nan ana samar da su a kasar nan ne da an samu ayyukan yi kimanin 100,000 a harkokin kananan kaji da talo-talo kadai.
Ya ci gaba da bayyana cewa “Shi ya sa hukumar tasu take goyon bayan rufe iyakar, kasancewar kawo yanzu yana haifar da da mai ido ga masana’antun noman kaji na cikin gida. A kan iya gano haka ne musamman ta karuwa tare da ingantattun kayayyakin noman kajin da kayayyakin adana su da sufuri da dai sauransu. Idan aka kuma yi la’akari da wadatattun abinci da aka samu a kasar nan daga noman kaji da dangoginsu musamman na shekarar 2016 da ya kai ton miliyan 5.3 wanda kashi 80 ciki an samu ne daga noman kaji a kasar da ke da yawan kimanin mutum miliyan 180 da kimanin ton na kwan kajin dubu 700 da ake samu a kowane shekara wato kimanin miliyan 450 na crates da kuma ton na nama da ya kai dubu 300. Ba shakka za a yi mamakin irin dubbai ko miliyoyin aiki da za a iya samu kai tsaye ta masana’antar da ire-irensa,” inji shugaban.