’Ya sanda sun kama mahaifina ne saboda ya daura min aure – ’Yar ASD
…Aure kan aure ta yi – Tsohon mijinta A farkon makon nan ne ’yan sanda a Jihar Kaduna suka kama fitaccen attajirin nan Alhaji Sani Dauda wanda aka fisani da ASD da Alkalin wata Kotun Shari’ar Mususlunci Malam Murtala Almisry da laifin daura aure kan aure. Har ila yau sun kama dan ASD mai suna Shehu […]
Daga hagu Alqali Almisry da xan ASD, Shehu Dauda sai mahafinsa Alhaji Sani Dauda (ASD)
…Aure kan aure ta yi – Tsohon mijinta
A farkon makon nan ne ’yan sanda a Jihar Kaduna suka kama fitaccen attajirin nan Alhaji Sani Dauda wanda aka fisani da ASD da Alkalin wata Kotun Shari’ar Mususlunci Malam Murtala Almisry da laifin daura aure kan aure.
Har ila yau sun kama dan ASD mai suna Shehu Sani tare da mahaifin nasu inda ake tsare su a hedkwatar ’yan sandan jihar, kafin a sake su a shekaranjiya Laraba.
An tsare su ne bisa sake aure da ’yar ASD mai suna Nasiba ta yi wanda tsohon mijinta bai ji dadin haka ba.
Alkali Murtala Almisry an tsare shi ne bisa zargin daura auren Nasiba da sabon mijinta a ranar Asabar da ta wuce shi kuma mahaifinta saboda amincewa da ya yi ’yarsa ta sake aure.
Wata majiya ta ce tsohon mijin nata wanda yana da alaka da Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya ne ya sa aka kama su.
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Kaduna, DSP Yakubu Sabo ya bukaci a ba shi lokaci ya bincika domin sanin hakikanin abin da ya faru kafin ya ce wani abu.
Amma lauyan ASD, Madwell Kyon ya bayyana wa manema labarai a ranar Talata, cewa sun samu nasarar samun oda daga kotu ta a sake wadanda aka kama, kuma kada a sake kama su har sai an saurari karar.
Ya ce ya riga ya aike wa Sufeto Janar na ’Yan sandan da kuma Kwamishinan ’Yan sandan Jihar kwafin wannan oda da kotu ta bayar domin a sako wadanda ake tsare da su.
“Kotu babu abin da za ta yi iya yi maka saboda akwai son zuciya a cikin wannan zance. Mutum ne ya aurar da ’yarsa bayan ta je kotu ta nemi a raba aurenta da tsohon mijinta. Kotu kuma ta amince da wannan bukata aka kuma umarce ta da ta biya mijin wata dukiya ta kuma biya shi. Aka raba aure sannan tana da takardar shaidar an raba auren. Saboda haka batun wai an yi aure a kan aure ba gaskiya ba ne,” inji shi.
A jawabin Nasiba ta shaida wa BBC cewa aurensu ya mutu shekara biyu da suka gabata inda tuni ta gama idda.
“Aurena da shi babu domin sai da aka sa na rantse da Alkur’ani har alkalin ya zartar da hukunci aka gabatar min da shaidar mutuwar aure.”
Da wannan shaidar ce aka dogara wajen daura mata sabon aure da wani mijin. Amma ba a jima ba sai ’yan sanda suka kama magabatanta, ciki har da mahaifinta da alkalin kotun da ya daura mata auren.
Alkali Nasir wanda ya tabbatar wa BBC ya daura wa yarinyar sabon aure bayan ganin shaidar mutuwar aurenta na farko, ya ce wannan ne dalilin da ya sa ’yan sanda suka kama su.
Sai dai a cewar mijinta na farko Abubakar Musa Abubakar, kamar yadda lauyansa, Barista Safyan Sa’idu Tambai ya bayyana, an daura auren ne a kan aurensa, saboda an soke hukuncin kotun da ta kashe auren, kuma akwai shari’a cikin shara’a da ya dabaibaye auren.
“Kotun sama ta soke hukuncin kotun farko da ta kashe aurenta don haka ta dawo a matsayin matar Abubakar,” inji Barista Tambai.