Ya sanya kwado da sakata a motarsa saboda gudun barayi
Wadansu mutane da dama suna kauce wa kai motarsu gyara gareji saboda gudun barayi. Wani direba da aka sakaya sunansa ya sanya wa motarsa kwado da sakata maimakon ya kai a gyara masa mabudin. Wani mai suna Thomas Godfrey, mai shekara 49 mai sana’ar hannu ne ya bayyana rahoton tare da daukar hoton motar a […]
Wadansu mutane da dama suna kauce wa kai motarsu gyara gareji saboda gudun barayi. Wani direba da aka sakaya sunansa ya sanya wa motarsa kwado da sakata maimakon ya kai a gyara masa mabudin. Wani mai suna Thomas Godfrey, mai shekara 49 mai sana’ar hannu ne ya bayyana rahoton tare da daukar hoton motar a lokacin da yake tuki zuwa birnin Barnet da ke Arewacin Landan.
Thomas mazaunin Bermondsey da ke Kudancin Landan ya ce, ya yi mamakin yadda wadansu suke da wani irin tunani na daban, kamar masu sakarci.
Thomas ya ce, abin da ya ba shi mamaki shi ne yadda direban motar ya manna leda a gurbin makullin kwadon da ya sa a motar saboda kada ruwa ya shiga cikin ramin. Da a ce kwado daya ya sanya a jikin motar maimakon sanya biyu.
Thomas ya kara da cewa, a lokacin da na ga abin da direban ya yi wa motarsa sai na fara tunanin wannan ai sakarci ne, sai daga bisani na yi tunanin abin al’ajabi ba ya karewa, kuma wannan direban zai iya yiwuwa yana da hujjar yin haka ga motarsa.
Direban ya kwaikwayi wani mai nishadantarwa da ake kira Mista Bean wanda yake sanya kwado a kofar motarsa a matsayin makullin zai inganta tsaron motarsa saboda gudun barayi.