Ya sanya wa jaririn da matarsa ta haifa a layin zabe sunan Janar Muhammadu Buhari

Wani magidanci da matarsa ta haihu a layin tantance masu zabe a Funtuwa Jihar Katsina ya sanya wa dan da aka Haifa sunan zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari. Matar mai juna biyu mai suna Rashida Sagir da ke zaune a unguwar Lungun Tsamiya Kwalbati Biyu da ke cikin garin Funtuwa ta haihu ne a […]

Ya sanya wa jaririn da matarsa ta haifa a layin zabe sunan Janar Muhammadu Buhari
Ya sanya wa jaririn da matarsa ta haifa a layin zabe sunan Janar Muhammadu Buhari

Wani magidanci da matarsa ta haihu a layin tantance masu zabe a Funtuwa Jihar Katsina ya sanya wa dan da aka Haifa sunan zababben Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari.

Matar mai juna biyu mai suna Rashida Sagir da ke zaune a unguwar Lungun Tsamiya Kwalbati Biyu da ke cikin garin Funtuwa ta haihu ne a lokacin da take kan layin tantace masu zabe a ranar Asabar da ta gabata da aka gudanar da zaben Shugaban kasa da sanatoci da ’yan majalisar wakilai.
Rashida wadda majiyarmu ta ce ta fita ne domin kada kuri’arta kuma tana cikin layi ne nakuda ta kama ta inda nan take sauran matan da ke wurin suka taimaka mata suka dauke ta zuwa wani wuri inda ta haifi namiji kamar yadda Aminiya ta samu labari.
Aminiya ta jiyo cewa mijin Rashida, Malam Sagir ya nuna farin ciki, inda ya yi wa Allah godiya da matarsa ta sauka lafiya kuma a wajen kwato wa kanta da jama’a hakki da nuna kishi ga kasarta ta hanyar zaben wadanda take so su shugabance ta.
Majiyar ta ce Malam Sagir bai yi wata-wata ba, ya yi wa dansa huduba kuma ya rada masa sunan Janar Muhammadu Buhari, ko kalmar Janar din bai cire ba. Ya yi fatan alheri ga dansa da matarsa Rashida tare da yi mata fatan alheri da koshin lafiya. Har wa yau Sagir ya yi godiya ga dukkan wadanda suka taimaka wa matarsa a lokacin da take kokarin haihuwa.
A waje daya kuma wani mai suna Isa Idris ya rasa ransa a sanadiyyar tashin wata tarzoma a Kwakwaren Sheme ta karamar Hukumar Faskari a tsakanin magoya bayan Jam’iyyar APC da PDP a lokacin da ake gudanar da zaben. Kamar yadda Aminiya ta kalato daga wadanda suka shaida yadda al’amarin ya faru da suka nemi a sakaya sunayensu, sun ce, rikicin ya faru sakamakon zargin Isa da karbar katunan zaben wadansu mutane inda aka nemi da ya mayar wa kowa da katinsa saboda ba shi da dalilin karbar katunan.
Shaidun sun ce, kin bayar da katunan da Isa ya yi da ake zargi za a yi amfani da su ne don yin magudi, ya janyo tayar da jijiyoyin wuya da hatsaniya har ta kai ga rasa ransa.
A hira da gidan rediyon Jihar Katsina kai-tsaye, Mataimakin Gwamnan Jihar wanda dan asalin karamar hukumar ce, kuma dan takarar kujerar sanata daga shiyyar Funtuwa a Jam’iyyar PDP, Barista Abdullahi Garba Faskari ya bayyana rashin jin dadinsa kan hayaniyar da aka yi, inda ya yi kira a zauna lafiya.
Mataimakin Gwamnan ya ce, ya urmarci Jami’in ’Yan sandan yankin (DPO) ya yi bincike kan musabbabin rikici.
Tun daren jajibirin zaben ne aka samu rashin jituwar a tsakanin magoya bayan jam’iyyun biyu a garin ’Yankara, amma aka shawo kanta ba tare da an kai ruwa rana ba.