Ya sayar da gida da kamfaninsa don ya kewaya duniya da ’yarsa

Wani uba a kasar Sin ya sayar da gidansa da kamfaninsa, don kawai ya zagaya da ’yarsa ‘’yar shekara biyu ta ga duniya na tsawon shekara biyar. Labarin wannan uba mai suna Zhu Chundie ya ja hankalin duniya, musamman masu mu’amala da shafukan sadarwa na facebook.  Shafin sadarwar 163.com ya ruwaito yadda Zhu Chundie, mahaifin […]

Ya sayar da gida da kamfaninsa don ya kewaya duniya da ’yarsa
Ya sayar da gida da kamfaninsa don ya kewaya duniya da ’yarsa

Wani uba a kasar Sin ya sayar da gidansa da kamfaninsa, don kawai ya zagaya da ’yarsa ‘’yar shekara biyu ta ga duniya na tsawon shekara biyar. Labarin wannan uba mai suna Zhu Chundie ya ja hankalin duniya, musamman masu mu’amala da shafukan sadarwa na facebook. 

Shafin sadarwar 163.com ya ruwaito yadda Zhu Chundie, mahaifin wata karamar yarinya ‘’yar shekara biyu ya sha salwashin zagayawa da ita cikin duniya har na tsawon shekara biyar. Don haka ya sayar da gidansa da kamfaninsa, ranar Asabar din makon jiya.
Wata shida da suka gabata ya fahimnci cewa mafi yawancin abokansa suna aiki tukuru, amma bas u da isasshen lokacin zama da ’ya’yansu. Ganin haka sai kawai ya sayar da kadarorinsa, ya kuma yi shiri na wata uku. Ya kuma yi shawara da matarsa. Daga nan sai Zhui ya sayi mota kirar Rb, ya fara zagaya duniya tare da ’yarsa.
“Kasancewar uba kusa da yaro a lokacin yarinta na da matukar muhimmanci,” a cewar Zhu, inda ya yi nuni da cewa, ya san Rb ba ta kai gida jin dadin hutu ba. Sai dai Zhu na gani yin tafiye-tafiye da ’yarsa, don ta ga duniya yana da alfanu. Jaridar China daily ta bayyana cewa labharin ya dauki hankali mutane a kasar Sin fiye da yadda masu wankin tufafinsu a gabar mashigin rowan Wanzhou da ke Chongking suna gurbata ruwa; da kuma masu gasar tsere, wadanda ke daukar hankalin masoyansu, musamman in sun sanya tufafi irin na shugabannin addini.