Ya sayar da kodarsa ya sayi wayar iPhone, daya kodar kuma ta daina aiki
Bayan sayen iPhone 4 da kudin kodarsa da ya sayar a boye, wadda ta rage masa ta tsaya.
Wani saurayi mai suna Diao Wang wanda ya sayar da kodarsa daya don ya sayi wayar salula kirar iPhone 4, lokacin da yake shekara 17, ya samu kansa a tsaka-mai wuya, bayan da daya kodar tasa ta daina aiki.
Matashin ya yi haka ne saboda ba zai iya biyan kudin wayar a lokacin ba. Kuma bayan cire kodar an fada wa Wang cewa zai iya yin rayuwa ta yau da kullun da koda daya.
- Yara 775,000 sun daina zuwa makaranta a Katsina saboda rashin tsaro
- ’Yan sa kai sun kashe liman yana sallah da wasu mutum 10 a Sakkwato
Amma kusan bayan shekara takwas, inda a yanzu yake da shekara 24, ya samu nakasa ta dindindin bayan sayar da kodar, inda a yanzu yake dogara da na’urar da likita ya sanya masa a jiki don ta rika aikin kodar saboda dayar da ta rage masa ba ta yin aiki.
A shekarar 2011, waya kirar iPhone 4 ce babbar wayar salula wadda Kamfanin Apple ya kera kuma ta shahara a makarantar su Diao Wang da ke Chengzhou a kasar China.
Matashin ya sha alwashin ko ta wane hali sai ya mallaki wayar duk da ya fito ne daga gidan talakawan da ba za su iya saya masa ita ba.
Wannan ne ya sa ya yanke shawarar sayar da kodarsa daya mai lafiya don samun kudin da zai iya sayen wayar.
Tare da taimakon wani mai shiga tsakani, Wang ya hadu da wani wanda ya kware wajen kasuwancin sassan jikin dan Adam ta haramtacciyar hanya.
Hakan ya sa ya amince ya sayar da kodar a kan kudin China Yuan 22,000 (Dala 3,200, daidai da Naira miliya daya da dubu 311 da 232).
An yi tiyatar cire kodar ce a wani haramtaccen asibiti a Chenzou, kuma duk da cewa an yi nasarar yin aikin, daga bisani matsalolin rashin lafiya sun taso masa ba da dadewa ba.
Abu mafi muni shi ne dangin Wang ba su da masaniya game da sayar da kodar, inda suka gano hakan a lokacin da matashin ya ga ba zai ci gaba da boye dalilin rashin lafiyarsa ba.
Tun daga wancan lokaci ne Diao Wang ya fara kashe mafi yawan lokacinsa a kan gado, saboda ya dogara ga na’urar wanke koda (dialysis) wadda take taimaka masa wajen gudanar da rayuwarsa.
Za a iya cewa, wadansu sukan sa rayuwarsu a cikin hadari sanadiyyar son abin duniya, sannan akwai abubuwa da suke jawo aukuwar hadari a rayuwar mutum, amma tabbas wayar tarho kirar Apple iPhone ba ta cikin jerinsu.