Ya sayar da ’yarsa don jana’izar surukarsa
A ranar Litinin din da ta gabata ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas Mista Imohimi Edgal ya gabatar wa ’yan jarida wadansu da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban cikin har da wanda ya sayar da ’yarsa mai shekara daya domin ya samu kudin binne surukarsa. Mututmin mai shekara 37 mai suna Kingsley Oriaku, ya […]

A ranar Litinin din da ta gabata ce Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Legas Mista Imohimi Edgal ya gabatar wa ’yan jarida wadansu da ake zargi da aikata laifuffuka daban-daban cikin har da wanda ya sayar da ’yarsa mai shekara daya domin ya samu kudin binne surukarsa.
Mututmin mai shekara 37 mai suna Kingsley Oriaku, ya shiga hannun ’yan sanda ne saboda zarginsa da sayar da ’yarsa mai shekara daya, mai suna Nkechi a kan Naira dubu 190, kuma daga baya ya sace wani dan makwabcinsa mai shekara bakwai ya sayar da shi a kan Naira dubu 120.
Makwabtan wanda ake zargin ne suka kai kara ga ’yan sanda bayan bacewar dan makwabcinsu, inda rundunar ta sake bin sawunsa a Jihar Abiya inda ya kai su ya sayar suka yi sa’ar samun yaron aka taso keyarsa.
Ana zargin Kingsley Oriaku ya sayar da ’yarsa ce kimanin wata biyu da suka shude, daga bisani kuma ya sace dan maƙwabcinsa ya sayar.
Rahotanni sun ce Kingsley Oriaku ya sayar da yaran biyu ne ga wata jagorar wani coci a Jihar Abiya.
Kafin ya sace dan makwabcinsa ya shaida wa makwabtansa cewa yana son ya saya wa yaron wani abu ne inda ya gudu da shi.
Wanda ake zargin ya shaida wa Aminiya cewa shi magini ne kuma bayan da surukarsa ta rasu ya shiga zullumin yadda zai tara kudin da za a binne ta domin abokan huldarsa sun rike masa kudin da yake bin su bashi, hakan ne ya sanya ya dauki karamar ’yarsa ya sayar wa jagorar cocin, “a lokacin da na kai wa jagoran cocin ’yar tawa na roke ta da kada ta sayar wa wadanda za su kashe ta, sai ta ba ni tabbacin cewa za a ajiye ta a gidan marayu,” inji shi.
Ya ce bayan ya sayar da ’yarsa da kwana biyu ne ya dawo Legas ya dauki dan makwabcisa ya tafi da shi Abiya ya sayar. Ya ce, “Bayan kwana biyu, sai na dana tarko ga dan makwabcina cewa zan saya masa alawa, na sa ya biyo ni da yamma. Nan da nan muka bar gidanmu da ke unguwar Meiran, na wuce da shi tashar mota inda na hau mota da tsakiyar dare zuwa Abiya.”
“Na kira mai gidan marayun kafin in bar Legas tare da dan makwabcina. Mun shirya za ta saye shi a kan Naira dubu 190, amma abin mamaki da na isa Umu’ahiya da ke Jihar Abiya, sai ta ce Naira dubu 120 kawai za ta iya biya a kan yaron,” inji shi.
“Da wannan, kudin ya kama Naira dubu 310 na ba da gudunmawar binne surukata, daga baya matata ta matsa mini a kan maganar ’yarmu sai na fada mata gaskiyar lamarin da ya faru inda ta shigar da kara a ofishin ’yan sanda na Meiran, inda na kai su inda na yi cinikin ’yar tamu aka sasanta muka karbo ta,” inji shi.
Oriaku ya ce: “Na san abin da na aikata bai dace ba, amma a lokacin na rikice ne kuma na shiga cikin damuwa. Matata ita ce babba kuma ’ya tilo, kuma lokacin da mahaifiyarta ta rasu a watan Satumba, surukaina sun bukaci kudi mai yawa daga gare ni.”
’Yan sanda sun ce, wanda ake zargin ya amince da laifinsa, inda ya shaida musu cewa ya rikice ne kuma ya shiga damuwa kan yadda zai binne surukarsa.
Kwamishina Imohimi Edgal, ya ce ’yan sanda sun bibiyi rahoton bacewar yaron ne da wani mai suna Olabisi Yanga ya gabatar musu a watan Oktoba inda suka kai ga nasarar kama wanda ake zargin.