Ya sha alwashin dawo da martabar jam’iyyar PDP
Daya daga cikin masu neman zama shugaban jam’iyar PDP na kasa baki daya, tsohon Ministan Wasanni da Ayyukan Musamman, Farfesa Taoheed Adedoja ya ce ziyarar ganawa da tsofaffin shugabannin kasa da yake yi a yanzu za ta taimaka masa wajen samo hanyar hada kan miliyoyin magoya bayan jam’iyyar, ta yadda za su iya karbar mulki […]
Daya daga cikin masu neman zama shugaban jam’iyar PDP na kasa baki daya, tsohon Ministan Wasanni da Ayyukan Musamman, Farfesa Taoheed Adedoja ya ce ziyarar ganawa da tsofaffin shugabannin kasa da yake yi a yanzu za ta taimaka masa wajen samo hanyar hada kan miliyoyin magoya bayan jam’iyyar, ta yadda za su iya karbar mulki cikin ruwan sanyi a zaben 2019 mai karatowa.
Da yake zantawa da ’yan jarida bayan wata ganawa da tsohon Shugaba kasa Olusegun Obasanjo a gidansa da ke Abekuta, dan siyasar, wanda dan asalin birnin Ibadan ne kuma haifaffen Kano ya ce: “Duk da yake tsohon Shugaba Obasanjo ya tsame hannunsa daga harkokin siyasa amma a matsayina, na mai son zama shugaban jam’iyar hamayya ta PDP, ya zama wajibi mu nemi shawarar irin wadannan tsofaffin shugabanni kamar shi kansa Olusegun Obasanjo da Ibrahim Babangida da Goodlock Jonathan da Abdulsalam Abubakar da Shehu Shagari da Shonekan, domin da tsohuwar zuma ake magani.”
Da yake amsa wata tambaya ya ce a tattaunawar da suka yi da Obasanjo, ya yi ta ambaton irin mutane da suka samu shaidar gaskiya da rikon amana da adalci da karbuwa a sassa daban-daban na kasa, wadanda yake cewa su ne za su iya rike ragamar jagorancin PDP da zai kai ga dorewar dimukradiya a Najeriya.
A game da fafatawar da yake yi da wasu jiga-jigan PDP a sashen Kudu maso yamma, sai ya ce, “ni dai na dogara ga Allah wajen fitowar neman zama shugaban PDP na kasa, zan yi aiki da dukkan mikakkiyar hanyar da ta dace wajen fafutukar neman wannan kujera. Ba zan yi amfani da siyasar bangaranci da banbancin addini ko kabila ba. Idan Allah Ya sa na zama shugaban PDP na kasa baki daya zan yi amfani da gogewar da na yi da irin karbuwar da na samu a sassa daban-daban na kasa wajen dawo da martabar jam’iyyar.