Ya shawarci al’ummar musulmi da kirista kan muhimmancin zaman-tare
Wani malamin addinin Musulunci na kungiyar Izalatul bidi’a wa ikamatussunna, reshen Jihar Edo, mai suna Ustaz Usman Kanawi ya yi kira tare da ba da shawara ga al’umman Musulmi da Kirista a kan muhimmancin zaman-tare da hadin kai da fahimtar juna a kan abubuwan da ke ci gaba da faruwa a cikin kasar nan. Ya […]
Wani malamin addinin Musulunci na kungiyar Izalatul bidi’a wa ikamatussunna, reshen Jihar Edo, mai suna Ustaz Usman Kanawi ya yi kira tare da ba da shawara ga al’umman Musulmi da Kirista a kan muhimmancin zaman-tare da hadin kai da fahimtar juna a kan abubuwan da ke ci gaba da faruwa a cikin kasar nan.
Ya bukaci bangarorin biyu da su rika lura da abin da ka je ya komo, musamman dangane da rabewar da ake yi da addini ko siyasa, a aiwatar da wasu abubuwan da ba su dace ba. Saboda haka ya nemi a rika kai zuciya nesa, ana gane manufa, domin babu abin da ya kai zaman lafiya dadi kuma babu abu mafi muni irin tashin hankali da fitina a kasa.
Furucin hakan ya fito ne a wata hira da malamin ya yi da Aminiya a garin Benin, inda ya ci gaba da cewa, “Lokaci ya yi da kowane dan Najeriya, musulmi da kirista za su hada kansu wuri guda su ceci kasar nan daga irin bala’in da take ciki. Lallai ne mabiya addini na gaskiya, Musulmi da Kirista su gane muhimmancin zaman lafiya da ribarsa.
A karshe ya roki Allah Ya kawo tabbataccen zaman lafiya a kasar nan gaba daya, sannan ya bukaci shugabanni su ji tsoron Allah su kwatanta gaskiya, su yi adalci cikin aikinsu na shugabancin al’umma da Allah Ya dora musu, domin Zai tambaye su kan haka ranar tashin alkiyama.