Ya shawarci Fulani mazauna Edo

Mashawarcin Gwamnan Jihar Edo kan Harkokin da suka shafi Al’ummar Arewa mazauna jihar Alhaji Sahabi Aliyu, ya bayyana bukatar da ke akwai ta Fulani makiyaya su ba gwamnatin jihar hadin kai da goyon baya, domin samun bakin zaren warware matsalolin da suke fama da su. Mashawarcin Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wani taron […]

Ya shawarci Fulani mazauna Edo
Ya shawarci Fulani mazauna Edo

Mashawarcin Gwamnan Jihar Edo kan Harkokin da suka shafi Al’ummar Arewa mazauna jihar Alhaji Sahabi Aliyu, ya bayyana bukatar da ke akwai ta Fulani makiyaya su ba gwamnatin jihar hadin kai da goyon baya, domin samun bakin zaren warware matsalolin da suke fama da su.

Mashawarcin Gwamnan ya yi wannan furucin ne a wani taron shugabannin Fulani da  a makon jiya, inda aka  tattauna tare da tabo batutuwa da dama, ciki har da batun tsaro. Ya ce muddin wasu mutane ko wata al’umma suna boye miyagu a cikinsu, ba a rabuwa da matsala saboda haka ya ce: “Ya zama wajibi a rika fallasa masu miyagun ayyuka ba tare da nuna batun ’yan uwantaka ko wata abota ba. Saboda haka wajibi ne ku shugabannin Fulani makiyaya ku tashi tsaye ku nuna da gaske kuna son gwamnati da hukumar tsaro a jihar nan su taimaka muku a kakkabe masu bata muku suna ko sun kasance ’ya’yanku ne. Ku hada kanku da gwamnati domin kare muku rayuka da dukiyoyinku.”
Daga nan sai ya ce: “Tunda akwai kungiyar Miyetti Allah ta kasa, wannan dama ce a gare ku, ku tashi tsaye tare da karfin gwamnati a kan zakulo miyagu masu bata muku suna a cikinku. Don haka ya kamata a ce a matsayinku na shugabanni, ku tashi tsaye ku tsaida gaskiya da tsananta bincike domin zakulo miyagun da mika su ga hukuma. Ina tabbatar muku cewa gwamnati za ta taimaka muku.”
Ya ce: “Ina kara nanata muku tare da shawartarku ku kasance masu daura damara, duk lokacin da kuka ga wani barawo ko wani mugu ya shigo muku; kada ku yi wani sako-sako, ku hanzarta sanar da hukuma. Wannan zai kara muku kwarjini, ku samu ku kakkabe duk wani mugu, amma idan kuka nuna kuna kaunarsu ko za ku kare su domin kasancewarsu ’ya’yanku, to lallai za a dauke ku tamkar ku kuke goya musu baya.”