Ya shawarci iyaye su kai yaransu makaranta

Wani Ardon Fulani ya kalubalanci iyaye da shugabanni a kan gurbacewar tarbiyyar matasan Fulani makiyaya, inda ya yi bayani da cewa laifin daga iyaye ne, wadanda idan aka auna abin da suke aikatawa a cikin jama’arsu ba karamar barna suke yi ba kuma ba komai ne ya haifar da hakan ba illa rashin ilimi.Ardon mai […]

Ya shawarci iyaye su kai yaransu makaranta
Ya shawarci iyaye su kai yaransu makaranta

Wani Ardon Fulani ya kalubalanci iyaye da shugabanni a kan gurbacewar tarbiyyar matasan Fulani makiyaya, inda ya yi bayani da cewa laifin daga iyaye ne, wadanda idan aka auna abin da suke aikatawa a cikin jama’arsu ba karamar barna suke yi ba kuma ba komai ne ya haifar da hakan ba illa rashin ilimi.
Ardon mai suna Muhammadu Mogaranji, ya yi bayyana hakan ne a wata tattaunawa da Aminiya a cikin makon da ya gabata a garin Benin, fadar mulkin Gwamnatin Jihar Edo. Ya shawarci shugabanni da iyayen yara na al’ummar Fulani makiyayan da su tashi tsaye su tabbatar suna kai ’ya’yansu makarantar boko da ta addini.
“Shawarar da zan ba shugabannin Fulani da iyayen yara ita ce, tun da farko su kasance masu halayya takwarai kuma iyaye su kuma su rika tura ’ya’yansu makaranta.” Inji shi.
Mogaranji ya tabo batun tsaro, inda ya ce: “Ina ganin tsaro yana inganta, idan al’ummar kasa suka hada kai suka ba gwamnati goyon baya.” Ya sake nanata bayaninsa da a kan batun tarbiyyar yara matasa. Ya ce “Ina sake nanata batun maganar sa ido a kan tarbiyyar yara, don haka wajibi ne iyaye su tashi tsaye wajen tura ’ya’yansu zuwa makaranta; domin ina ganin rashin ilimi ya taimaka wajen gurbatar tarbiyyar yaran Fulani.”