Ya shawarci matasa a kan su rungumi sana’o’i

Lokaci ya yi da matasan kasar nan za su tashi daga barcin gafala da mutuwar zuciya da suke a kai, su watsar da al’adar dora wa iyaye larurar kansu sai abin da suka yi musu, alhali su ba su tabuka komai na amfanin kansu. Irin wannan dabi’ar ba wadda za ta kawo ci gaba ga […]

Ya shawarci matasa a kan su rungumi sana’o’i
Ya shawarci matasa a kan su rungumi sana’o’i

Lokaci ya yi da matasan kasar nan za su tashi daga barcin gafala da mutuwar zuciya da suke a kai, su watsar da al’adar dora wa iyaye larurar kansu sai abin da suka yi musu, alhali su ba su tabuka komai na amfanin kansu. Irin wannan dabi’ar ba wadda za ta kawo ci gaba ga al’ummar kasa ba ce, don haka akwai bukatar su tashi su rungumi sana’o’i da za su amfani kansu da iyayensu da sauran al’ummar kasa.
Bukatar hakan ta fito ne daga bakin wani dan kasuwa a garin Benin Jihar Edo, Alhaji Idi Ma’azu  a wata hira da ya yi da wakilin Aminiya a karshen makon jiya.
 Alhaji Idi Ma’azu ya ce akwai rufin asiri ba kadan ba a yin sana’a ko da kankanuwa ce, amma wani abin mamaki wasu da dama ko da suna sana’ar ma sai ka taras da su suna yi mata rikon sakainar kashi yayin da wasu suke yawo ba su damu da mene ne za su yi na kare mutuncin kansu ba, musamman matasa masu son su ga sun samu komai a banza.
“Yau a kasar nan idan ka duba irin yadda matasa na wannan zamani suke sakarkancewa, sai yawon gararamba da irin wani zama na tsere sa’a maras amfani, babu baki kuma babu fari, sun fi son su ga suna ci a huce ba tare da sun tashi sun nuna wani kwazo ba ko yin wata sana’a da za su amfani kansu ballantana su amfani iyayensu da sauran mutanen kasa, sai abin ya ba ka takaici.”
Ya kara da cewa abin takaici ne da za ka gani matasanmu suna kokarin kutsa kai cikin aikin bangar siyasa, wasu kuma suna nan mutuwar zuciya ta kai masu kololuwa sun kidime suna ci gaba da kwaciyar tsere sa’a da son banza da zaman kashe wando ta haifar masu shaye-shayen ababen maye mai raba su da hankalinsu da lafiyarsu. “Amma ni kam abin da na gani shi ne duk mutumin da ya rungumi sana’a yana ci gaba da yin ta tsakani da Allah babu ha’inci babu zamba, to lallai sai ya samu rufin asiri da bai yi tsammani ba a rayuwarsa domin ko ba komai zai ci ya sha, ya yi sutura har ya taimaka wa wasu mutane”.
Alhaji Mu’azu ya shawarci matasan da cewa batun aikin gwamnatin da suke hankoro, wannan jiran gawon shanu ne domin a yanzu haka mutane nawa suka kammala karatunsu na digiri, kai har da digirgir, amma kuma  ba su samu aiki daga gwamnatin ba. “Don haka matasa su tashi su kama sana’a, su watsar da ce wa suna jiran sai gwamnati ta dauke su aiki. Wannan ba zai haifar masu da da mai ido ba”. Inji shi.
Kuma da ya juya a bangaren gwamnati kuwa, shawara ya bayar ta yadda za a bi domin rage wa ’yan asalin kasar nan radadin tsadar rayuwa na talauci da suke fama da shi, musamman matasa. Ya ce ya kamata gwamnatocin kasar nan daga sama har kasa su yi wata hobbasawa a kakkafa masana’antu manya da kanana a ko’ina a cikin kasa, domin ta haka ne mutane za su samu madogara tare da samun walwala.
Ya ce, “Idan gwamnati ta yarda ta yi aiki da wannan shawara, lallai da yardar Allah sai mun ga canji mai amfani domin zai rage irin yawan zaman kashe wando da matasa suke fama da shi.
A karshe sai ya kara da shawartar matasan, musamman na karkara da su rungumi noma, musamman noman rani, maimakon tafiyar da suke yi ta ci rani da ke janyo masu cin mutunci tare da gallazawa na babu gaira babu dalili a wasu sassan kasar nan. “Ina kira ga matasa da su koma noman rani a duk lokacin da suka kammala na damina, domin noman rani yana da amfani, ba kadan ba, za su samu abin biyan bukata ta kansu har su biya wa wasu kuma kasa za ta samu bunkasar arziki da abinci”, inji shi.