Ya shawarci Musulmi su rika yi wa shugabanni addu’a
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen karamar Hukumar Zariya, Sheikh Muhammad Sani Yakubu ya bukaci al’ummar Musulmi su rika yi wa shugabanni addu’a don samun ci gaba mai ma’ana maimakon tsine musu. Sheikh Sani Yakubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a yayin taron kwamitin da’awa […]
Shugaban kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah reshen karamar Hukumar Zariya, Sheikh Muhammad Sani Yakubu ya bukaci al’ummar Musulmi su rika yi wa shugabanni addu’a don samun ci gaba mai ma’ana maimakon tsine musu.
Sheikh Sani Yakubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake amsa tambayoyin manema labarai a yayin taron kwamitin da’awa mai suna Lajnatud Da’awa na Zariya da kewaye ya shirya bita ga malamai masu gudanar da tafsirin azumin watan Ramadan a shiyya ta daya da ta kunshi kananan hukumomi takwas da ya gudana a Tsangayar Mulki na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Kongo, Zariya.
Malamin ya ce da’a shi ne aka san Musulmi da shi amma ba wulakanci ko tozarci ga shugabanni ba, ya ce zagin shugabanni yana haifar da wahala da lalacewar kasa, yayin da lizimtar yi musu addu’a ne babbar fa’ida a gare su da mabiya.
Sheikh Sani Yakubu ya kuma shawarci shugabanni su rika kamanta adalci tare bai wa kowa hakkinsa duk da cewa sun samu kasar a cikin mawuyacin yanayi.
Sai ya gargadi masu yin batanci ga Manzon Allah su guji yin haka, inda ya koka da abin da ya faru makonni biyu da suka wuce a gidan yarin Zariya, lamarin da ya ce duk Musulmin kwarai zai la’ance su tare da yin tir da takale-takalensu.
Shugaban Kwamitin Da’awar Malam Alkasim Aminu Umar ya ce an shirya butar ne bisa la’akari da fuskantowar watan Ramadan, domin a yi kokarin nuna wa malamai ingantataccen abin da ya zo cikin Alkur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) da kuma fahimtar magabatan kwarai, wato sahabbai da tabi’ai da wadanda suka biyo bayansu da kyautatawa.