Ya shawarci ’yan kasuwa su tausaya wa jama’a a Ramadan

Mai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara a kan harkokin addinin Musulunci Malam Zakariya’u Madu Yaldu, ya ce watan Ramadan wata ne na afuwa da sauki wanda ya kamata ’yan kasuwa Musulmi su yi rangwame a cikinsa.Malam Zakariya’u Madu Yaldu, ya bayyawa haka ne a zantawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, inda ya […]

Ya shawarci ’yan kasuwa su tausaya wa jama’a a Ramadan
Ya shawarci ’yan kasuwa su tausaya wa jama’a a Ramadan

Mai ba Gwamnan Jihar Kebbi shawara a kan harkokin addinin Musulunci Malam Zakariya’u Madu Yaldu, ya ce watan Ramadan wata ne na afuwa da sauki wanda ya kamata ’yan kasuwa Musulmi su yi rangwame a cikinsa.
Malam Zakariya’u Madu Yaldu, ya bayyawa haka ne a zantawarsa da Aminiya a ofishinsa da ke Birnin Kebbi, inda ya ce, Manzon Allah (SAW) ya yi horo ga ’yan kasuwa su tausaya a cikin watan Ramadan domin al’ummar Musulmi su samu sauki a wannan wata mai albarka. “An san kasuwa tana zuwa ne da tsada ko araha, amma babu dadi kan yadda wasu ’yan kasuwa suke boye abubuwan da aka fi bukata lokacin azumi domin su sayar da tsada saboda su ci kazamar riba, wannan halaka ce babba,” inji shi.
Ya ce watan azumi wata ne da ake son tausayawa da saukaka wa al’umma da taimako ta kowane fanni domin rabauta da lada mai yawa a wurin Allah wanda azumi naSa ne.
Sai ya bukaci jama’a su ci gaba da addu’o’i a wannan wata na Ramadan da nufin samun mafita daga cikin halin rashin tsaro da ake ciki a kasar nan baki daya.