Ya shawarci ’yan majalisa su guji zama ’yan amshin shata

Wani dan siyasa a Jihar Kebbi Alhaji Isa Assalafi ya shawarci ’yan Majalisar Tarayya da na jihar su guji zama masu dumama kujera, ko ’yan amshin shata da ba su iya cewa komai a majalisa sai na goyon baya.Alhaji Isa Assalafi, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Birnin Kebbi, […]

Ya shawarci ’yan majalisa su guji zama ’yan amshin shata
Ya shawarci ’yan majalisa su guji zama ’yan amshin shata

Wani dan siyasa a Jihar Kebbi Alhaji Isa Assalafi ya shawarci ’yan Majalisar Tarayya da na jihar su guji zama masu dumama kujera, ko ’yan amshin shata da ba su iya cewa komai a majalisa sai na goyon baya.
Alhaji Isa Assalafi, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da wakilinmu a Birnin Kebbi, inda ya kalabalanci sababbin’yan majalisar su kasance masu sauke nauyin da tsarin mulki ya dora musu wajen kawo kudirorin da za su inganta rayuwar mutanen da suka sha wahala wajen zabensu.
Ya ce su bai wa al’umma kwarin gwiwa wajen kulawa ko tsare unguwanni da garuruwansu daga miyagun abubuwan da suke faruwa, “Su kasance masu son ganin ana gudanar da harkokin gwamnati bisa gaskiya da rikon amana ban da handama da babakere. Su tabbatar ba su bari an kwace musu matsayinsu na masu ’yancin kansu daga bangaren zartarwa ba, tare da sanya ido a kan ayyukan da bangaren zartarwa ke yi,” inji shi.
Assalafi, ya tunatar da ’yan majalisar cewa ba gwamnati ta kawo su kan kujerunsu ba, talakawa ne suka zabe su, don haka ya kamata su ba maranda kunya, ba su tsaya fadan wajen rabon mukamai ko neman kwangila ba.

Gwamnoni ku magance talauci da rashin tsaro —Sarkin Musulmi 

Amarya ta yanke maƙogwaron ango a Kano

NAJERIYA A YAU: Masu nau’in jinin AS sun fi masu AA lafiya — Masana

ADC za ta ƙalubalanci hukuncin soke mata rajista