Ya shawarci ’ya’yan APC su rika samar wa matasa aiki
Mai neman tsayawa takarar dan Majalisar Tarayya daga mazabar Katagum a Jihar Bauchi karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Abdulhamid Ghali Maji ya shawarci masu takarar neman mukamai a jam’iyyar a sassan Najeriya su himmatu wajen kula da lafiya ga marasa karfi tare da sama wa matasa aikin yi domin komai ya tafi daidai a kasar nan.Alhaji […]
Mai neman tsayawa takarar dan Majalisar Tarayya daga mazabar Katagum a Jihar Bauchi karkashin Jam’iyyar APC, Alhaji Abdulhamid Ghali Maji ya shawarci masu takarar neman mukamai a jam’iyyar a sassan Najeriya su himmatu wajen kula da lafiya ga marasa karfi tare da sama wa matasa aikin yi domin komai ya tafi daidai a kasar nan.
Alhaji Abdulhamid Ghali Maji ya bayyana haka ne a wajen kaddamar da shirinsa na inshorar kiwon lafiya karo na biyu ga mutum 200 da aka yi a garin Azare.
Alhaji Ghali Abdulhamid ya ce, ya fito da shirin ne domin tallafa wa mutanen da suke fama da cututtuka
na tsawon lokaci ba tare da samun waraka ba, saboda rashi da ake fama da shi.
Ya kara da cewa a kwanakin baya ya kaddamar da shirin farko ga mata 100, a yanzu ya kaddamar da shirin ga maza 100, inda ya ce ya ware kudi ya bayar a Cibiyar Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Azare, inda za a ba da kati ga wadanda suka ci gajiyar shirin don ganin likita da magani ko tiyata kyauta.
Alhaji Ghali Maji ya ce ya yi haka ne domin a wasu lokuta idan aka bayar da kudi domin wannan aiki bai cika isa ga wadanda aka yi dominsu ba, kuma akwai masu sa ido kan lamarin ta yadda duk wanda aka yi dominsa ba zai ci karo da wata matsala ba.