Ya shekara 16 yana kwana daki daya da gawar matarsa
Wani mutumin kasar Vietnam mai suna Mista Le Ban, ya shafe shekara 16 yana kwana daki daya da gawar matarsa sakamakon shakuwar da ya yi da ita. Lokacin da aka fara samun rahoton cewa Mista Le Ban, yana kwana daki daya da gawar matarsa a shekara 2009, wadansu da dama suka yi ta karyata rahoton, […]
Wani mutumin kasar Vietnam mai suna Mista Le Ban, ya shafe shekara 16 yana kwana daki daya da gawar matarsa sakamakon shakuwar da ya yi da ita.
Lokacin da aka fara samun rahoton cewa Mista Le Ban, yana kwana daki daya da gawar matarsa a shekara 2009, wadansu da dama suka yi ta karyata rahoton, amma daga bisani aka tabbatar da haka.
Rahotanni sun ce, wani mutum ya je kabarin matarsa ya hako ta ya dauke ya tafi da ita gida, inda daga baya aka tabbatar da cewa Mista Le ne ya aikata haka shekara 16 da suka gabata duk da alhinin da ’yan uwansa suka nuna game da rashin matar.
Mista Le, ya auri matarsa ce a 1975, kuma ba su san juna ba kafin aurensu, inda aka ce iyayensu ne suka hada auren tun suna yara. Kuma bayan Mista Le ya dawo daga aikin soja yana matashi ne aka yi daura auren.
Bayan auren sun rayu cikin annashuwa da jin dadi. Sun haifi ’ya’ya bakwai, kuma wata rana a shekarar 2003, lokacin Mista Le yana aiki nesa da garinsu, sai ya samu labarin rasuwar matarsa. Hakan ya sa ya hanzarta dawowa gida mintuna kadan kafin a binne ta.
Da farko kafin Mista Le, ya hako matarsa ya koma yana zama a makabarta dare da rana, wani lokacin ma yana kwanciya a kan kabarinta. Sakamamon canjin yanayi a damina, sai ya yanke shawarar hako gawar matar tasa daga cikin kabari don kasancewa tare da ita a koyaushe, daga nan ya fara kwanciya kusa da gawar. Ba a dade ba ’ya’yansu suka gano cewa Mista Le, ya daina zuwa makabartar.
Wani dare ne Mista Le, ya yanke shawarar daina kwanciya a makabarta, ya kawo matarsa gida don ta kasance tare da shi, ya tone kabarin ya dauki gawar ya binne kasusuwanta, sai ya saka wasu sassan jikin a cikin wata jaka da ke kusa da makabartar.
Daga bisani, ya sassaka gunkin matar ya hada da siminti da kasa ya manne tare sauran sassan jikin gawar.
Hakan ya sa koyaushe yake tare da gawar, da ya yi wa ado har tsawon shekara 16. Da ’ya’yan Mista Le, suka fahimci abin da ke faruwa, sai suka bukaci mahaifin nasu ya mayar da gawar mahaifiyar tasu cikin kabarinta. Sai dai Mista Le, ya ce ba zai iya rayuwa ba tare da gawar matarsa ba.
Makwabtan Mista Le, sun kai shekaru ba su ziyarci gidansa ba, saboda sun samu labarin ya hako sassan gawar matar ya dawo da su gida, kuma wadansu sun ce, an sanar da hukuma kan zargin yana yada cututtuka.
’Yan sanda sun yi kokarin gamsar da Mista Le kan ya mayar da gawar matarsa zuwa kabarinta, amma duk da haka ya ki.
“Jama’ar kauyen sun umarci Mista Le, ya binne matarsa kuma ya amince da yin hakan. Bayan wani lokaci sai makwabtansa suka gano bai aikata hakan ba, ya bar gawar a dakinsa, saboda tsatstsauran ra’ayi ya yi watsi da bukatunsu,” inji Mista Tran Trong Sanh, Shugaban Birnin Ha Lam, a tattaunawarsa da kafar labarai ta BietnamNet a shekarar 2005.