Ya shekara 30 yana haka kogi zuwa kauyensu

Wani dattijo kuma tsohon ma’aikaci da yanzu ke karbar fansho mai suna Laungi Bhuiyan, dan asalin kauyen Kothilawa a yankin Lahthua da ke Gundumar Gaya a Jihar Bihar ta kasar Indiya ya sadaukar da rayuwarsa ta hanyar haka magudanar ruwa da hannu shi kaxai mai tsawon kilomita uku, inda ya yi shekara 30 yana aikin […]

Ya shekara 30 yana haka kogi zuwa kauyensu

Mista Laungi Bhuiyan lokacin da yake aikin hakan

Wani dattijo kuma tsohon ma’aikaci da yanzu ke karbar fansho mai suna Laungi Bhuiyan, dan asalin kauyen Kothilawa a yankin Lahthua da ke Gundumar Gaya a Jihar Bihar ta kasar Indiya ya sadaukar da rayuwarsa ta hanyar haka magudanar ruwa da hannu shi kaxai mai tsawon kilomita uku, inda ya yi shekara 30 yana aikin haqar.

An fi sanin Laungi Bhuiyan da suna “Canal Man” (Mutum Mai Haqa Magudanar Ruwa) kauyen Kothilawa ya dade yana fama da karancin ruwa, duk da akwai wani ruwa da ke sauka daga saman dutse ya wuce wani kogin makwabtan kauye maimakon ya karasa kauyen.

Wannan ne dalilin da ya sa wadansu jama’ar garin suka fara kaura daga kauyen saboda karancin ruwa, sai suka yi nasarar samun jarumin dattijo Laungi Bhuiyan da ya kudiri niyyar magance matsalar da kauyen ke fama da shi, inda ya fara aikin samar da ruwa da ya kai shekara 30 yana yi, ta hanyar samar da ruwan daga wani tsauni zuwa wani kududdufi da ke kusa da kauyen.

Mista Laungi Bhuiyan

Tun lokacin da ya fara aikin bai nemi agajin kowa ba a kauyen har tsawon shekara 30 da ya kwashe yana haka hanyar ruwan mai fadin kafa 4 da zurfin kafa 3 da kuma abin hakar da yake amfani da shi da hannunsa.

Laungi Bhuiyan ya bayyana cewa, “Na shekara 30 ina hakar hanyar ruwa zuwa kududdufin kauyenmu,” ya bayyana wa kafar labarai ta ANI.

“Shekara 30 da suka gabata ina fitowa kiwo da shanuna, daga nan na fara haka hanyar ruwan. Ba wanda ya taimaka min wajen aikin, sanadiyyar karancin ruwa kawai sai mazauna kauyen suka fara kaura zuwa birane, amma na yanke shawarar ci gaba da zama a kauyen don magance matsalar.”

Kauyen Laungi na da nisan kilomita 80 daga garin Gaya hedkwatar Kothilawa da ke kewaye da bishiyoyi musamman lokacin damina da kuma manyan duwatsu, yayin da ruwa ke gangarowa daga duwatsun kai-tsaye zuwa kogin kauyen.

Bayan hakar hanyar ruwan da Laungi ya yi aka fara samun ruwa, makiyaya da manoma suka daina yin korafin karancin ruwa a kauyen. Laungi ya haka hanyar ruwan inda mutane da dabbobi da yawa suke amfana da qoqarinsa na wadata kauyen da ruwa.

Kamar yadda wani mazaunin kauyen mai suna Patti Manjhi ya bayyana. Wani malamin makaranta a kauyen mai suna Ram Vilas Singh ya ce Laungi ya shahara a yankin saboda kokarin da ya yi ga jama’ar kauyen Masu bibiyar shafukan sada zumunta na zamani sun jinjina wa Laungi sakamakon ceto kauyensa da ya yi daga matsalar da ta yi sanadin sanya mazauna kauyen yin hijira.

Wadansu dai sun bukaci gwamnatin kasar ta saka masa kan irin kokarin da ya yi, don bai wa wadansu kwarin gwiwa yin abin alheri ga jama’a.