Ya shiga aikata laifuka domin tabbatar wa gwamnati yana raye

Abin mamaki, batun Baburam ba bakon abu ba ne a Indiya.

Ya shiga aikata laifuka domin tabbatar wa gwamnati yana raye

Wani ɗan kasar Indiya mai suna Baburam Bhil da gwamnati kasar ta bayar da takardar tabbatar da mutuwarsa ya shiga aikata laifuffuka a matsayin hanyar tabbatar wa gwamnatin cewa yana raye.

Baburam mai shekara 40 ɗan asalin garin Mithora na Jihar Rajasthan, ya daɗe yana kokarin nuna wa hukumomi cewa yana raye amma ba su amince ba.

Kuma bayan ya yi kokarin a gyara kuskuren tare da yin kira ga dattawan kauyensa da hukumomin jihar, abin ya ci tura, sai ya yanke shawarar ya nemi wani za&i mai tsauri.

Kuma ya yi haka ne saboda tsoron gwamnati za ta iya kwace dukkan kadarorinsa sakamakon mutuwarsa, inda Baburam ya yanke shawarar zama babban mai aikata laifi a matsayin hanyar jawo hankali a kan matsalarsa.

A ranar 19 ga watan Yulin bana, ya rike wuka da kwalbar fetur ya fara kai wa wata makarantar unguwa hari.

Bayan ya shiga Makarantar Chuli Bera Dharana, Baburam ya raunata malamai biyu da suka haɗa da Mataimakin Shugaban Makarantar, Hardayal da wani malami mai suna Suresh Kumar, da wasu iyayen ɗalibai.

A cewar rahoton ’yan sanda, Baburam Bhil ya kuma yi garkuwa da ɗalibai da malamai da dama sai da jami’an tsaro sun samu nasarar kama shi.

A yayin da ake yi masa tambayoyi, Baburam ya bayyana cewa an yi masa rashin gaskiya ne, kuma ya yi ta kokarin a soke takardar mutuwarsa, yana neman a tabbatar yana raye, amma aka ki.

Ya ce aikata manyan laifuffuka da za su iya sa a kama shi, zai sa ’yan sanda ba su da wani zabi da ya wuce su kama shi su rubuta sunansa a cikin bayanan ’yan sanda, wanda ke nuna cewa a zahiri bai mutu ba.

An kama Baburam Bhil saboda laifuffukan da ya aikata, amma shirin nasa na da manufa ce kawai, yayin da ’yan sanda suka sanar da gudanar da bincike a kan ikirarinsa.

Abin mamaki, batun Baburam ba bakon abu ba ne a Indiya.

Jaridar Vio News ta ruwaito cewa, a watan Nuwamban bara, an ga wani mai shekara 70 yana tafiya ta hanyar Agra ɗauke da wani rubutu mai suna ‘Ina raye’ bayan an ba da takardar shaidar mutuwarsa bisa kuskure.