Ya shiga cikin rijiya mai zurfi don ceto maciji
Wani mutum da ke aiki a wani gandun daji mai suna Shagil da ke kauyen Peramangalam a gundumar Thrissur a Jihar Kerala da ke kasar Indiya, ya shiga cikin wata rijiya mai zurfi don ceto wani maciji da ya fada. Shagil, ya shiga cikin rijiyar ce tare da wata igiya da za ta taimaka masa […]
Wani mutum da ke aiki a wani gandun daji mai suna Shagil da ke kauyen Peramangalam a gundumar Thrissur a Jihar Kerala da ke kasar Indiya, ya shiga cikin wata rijiya mai zurfi don ceto wani maciji da ya fada.
Shagil, ya shiga cikin rijiyar ce tare da wata igiya da za ta taimaka masa wajen riko macijin don fito da shi.
Wani bidiyo da ke nuna lokacin da Shagil ke ceto macijin daga cikin rijiyar ya dauki hankalin jama’a da dama, saboda yadda ya yi amfani da igiya wajen fitowa daga cikin rijiyar tare da riko jelar macijin, sannan macijin ya nade jikin Shagil lokacin da yake kokarin fitowa da macijin waje.
A lokacin da Shagil ya kusa fita daga cikin rijiyar tare da macijin sai hannunsa ya kubce suka fada cikin rijiyar, a lokacin da suka fada hoton bidiyon bai bayyana abin da ya faru ba, tsakanin macijin da Shagil.
Rahotan ya tabbatar da cewa, Shagil mai ceton macijin tare da macijin duk sun kubuta daga rijiyar.
Shagil, ya bayyana wa kafar sadarwa ta Manorama News Channel cewa, “A lokacin da na ga macijin a cikin rijiyar, abin da ya fara zuwa min a rai shi ne, in kama ta hanyar wani tarko amma sai dai rijiyar na da matukar zurfi. Kuma a lokacin da muke kokari kama shi sai macijin ya ci gaba da tserewa, sai kawai na yanke shawarar fadawa cikin rijiyar tare da amfani da igiya, ina shiga cikin rijiyar sai macijin ya iso kusa da ni, daga nan sai na rike masa kai.”
Shagil, ya kara da cewa alokacin da ya kusan fitowa daga cikin rijiyar sai ya bukaci wani mazaunin kauyen ya rike masa hannu.
Da farkon rike macijin da Shagil, ya yi ya ji tsoro hakan ya sa duk suka fada cikin rijiyar. Shagil ya ce saboda zurfin rijiyar da kuma ruwa da yawa ya sa bai ji rauni ba, haka shi ma macijin.
Shi dai Shagil ya kasance yana da hikima wajen gudanar da harkokinsa da dabbobi, macijin bai kawo masa wata matsala ba. Sai dai kawai karamin kuskure da aka samu lokacin ceto macijin lokacin da ya bukaci wani ya rike masa hannu.
Bayan ceto macijin cikin koshi lafiya an sake shi zuwa cikin daji don ci gaba da rayuwarsa kamar yadda ya saba.