Ya shiga hannu kan zargin satar yarinya

Sashen bincike na rundunar ’yan sandan Jihar Legas suna bincikar wani Mamman, wanda ake zargin ya saci wata yarinya mai suna A’isha Hasan a unguwar Agege.Mahaifin yarinyar mai suna Alhaji Hasan Yahuza ya bayyana wa Aminiya cewa asirin mutumin ya tonu yayin da ya je makarantarsu ya yi kokarin sace ta.Ya ce, “Mutumin, wanda yake […]

Ya shiga hannu kan zargin satar yarinya

A’isha HasanSashen bincike na rundunar ’yan sandan Jihar Legas suna bincikar wani Mamman, wanda ake zargin ya saci wata yarinya mai suna A’isha Hasan a unguwar Agege.
Mahaifin yarinyar mai suna Alhaji Hasan Yahuza ya bayyana wa Aminiya cewa asirin mutumin ya tonu yayin da ya je makarantarsu ya yi kokarin sace ta.
Ya ce, “Mutumin, wanda yake da lalurar ido daya, ya je makarantar su A’isha ya kama hannunta ya fita da ita, sai wani da ke makwabtaka da makarantar ya hango shi, sai ya fadakar da malaman makarantar, wadanda nan da nan suka kama shi da suka yi masa tambayoyi, sai ya kasa bayar da amsa. Ni kaina da na tambaye shi, sai ya ce mini gida zai kai ta, alhalin bai taba ganinta ba kuma bai san gidanmu ba. Sai ya rika rokona na rufa masa asiri kuma ya rika nanata cewa taimaka mata zai yi, ba sace ta ba”.
Sai dai mutumin mai suna Mamman, mai kimanin shekaru 40, dan asalin garin Kanya, a karamar Hukumar Rano da ke Jihar Kano ya musanta zargin da ake yi masa, kuma jami’in ’yan sanda da ke kula ofishin unguwar Isekoko ya ki yarda a dauki hotonsa ko muryarsa a na’ura, saboda tsoron kada hedikwatarsu ta tuhume shi.
Shugaban makaranatar firamare ta Oniwaya, wanda ya ki yarda a dauki muryarsa ko hotonsa, ya ce ba shi da hurumin cewa komai kan lamrin, sai dai na tuntubi ’yan sanda.
Jami’in da ke kula da ofishin ’yan sanda na Isekoko ya ce ba zai ce komai ba, sai dai na tuntunbi mai magana da yawun ’yan sandan Jihar Legas.
Mai magana da yawun ’yan sandanm, Ngozi Braideta ta tabbatar da aukuwar lamarin, inda ta ce da zarar sun kamala bincike, za su gurfanar da wanda ake tuhuma a gaban kuliya.