Ya shirya kasaitacciyar walimar murnar dawowar Buhari daga Landan
Wannan ne dai karo na takwas da Rabi’u ke shirya irin wannan walimar inda yake yanka rago a duk lokacin da shugaban ya dawo
Wani dan-a-mutun Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya shirya wata kasaitacciyar walimar bude-baki domin murnar dawowarsa daga Landan wajen neman lafiya.
Da yammacin Juma’a ne dai matashin mai suna Rabi’u, wanda aka fi sani da Abu Albarka ya tara mutane a wani gidan sayar da abinci dake daura da Jami’ar Tarayya dake Dutsin-Ma a jihar Katsina domin walimar.
- ‘Ana yi wa ’yan Arewa kisan dauki dai-dai a Imo’
- JAMB ta haramta wa iyaye raka ’ya’yansu wuraren zana jarabawa
Wannan ne dai karo na takwas da Rabi’u ke shirya irin wannan walimar inda yake yanka rago a duk lokacin da shugaban ya dawo daga ketare musamman wajen neman lafiya.
Taron dai ya kuma sami halartar sauran ’yan-a-mutun Buharin yayin bude-bakin, inda suka yi addu’o’in ci gaban Najeriya da samun karin lafiyar shugaban.
“Akwai akalla mutum 40 da suka halarci taron, kuma wannan shine adadi mafi karanci kasancewar lokacin azumi ne. Na karshen da muka yi kafin wannan sama da mutum 300 ne suka halarta,” inji shi.
Abu albarka ya kuma ce Najeriya bata taba samun wata baiwa da ta kai ta samun Buharin a matsayin Shugaban Kasa ba, musamman a daidai lokacin da take fama da kalubalen tattalin arziki da ta matsalar tsaro.
Ya kuma yi kira ga sauran ’yan Najeriya da su ci gaba yi wa shugaban da kasa Najeriya addu’a domin samun ci gaba.
Shima a nasa jawabin, shugaban Kungiyar Masoya Buhari na duniya, Ibrahim Bature wanda shima ya ba da gudunmawa wajen shirya taron ya yi kira ga matasa da su shiga siyasa domin ba da tasu gudunmawar wajen ci gaban kasa.