Ya soki kungiyar CAN kan umartar Kiristoci su zabi dan takarar PDP a Taraba

Shugaban wata kungiyar matasa Musulmi da Kirista a Jihar Taraba Mista Jinaidu Garbey Yawe ya la’anci ikirarin da kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar ta yi cewa dan takarar Gwamnan Jihar na Jam’iyyar PDP Mista Darius Ishaku kadai Kiristoci za su goya wa baya a zabe mai zuwa. Mista Jinaidu Garbey Yawe ya ce […]

Ya soki kungiyar CAN kan umartar Kiristoci su zabi dan takarar PDP a Taraba
Ya soki kungiyar CAN kan umartar Kiristoci su zabi dan takarar PDP a Taraba

Shugaban wata kungiyar matasa Musulmi da Kirista a Jihar Taraba Mista Jinaidu Garbey Yawe ya la’anci ikirarin da kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen jihar ta yi cewa dan takarar Gwamnan Jihar na Jam’iyyar PDP Mista Darius Ishaku kadai Kiristoci za su goya wa baya a zabe mai zuwa.

Mista Jinaidu Garbey Yawe ya ce fidda dan takara daga cikin ’yan takarar Gwamna a jihar a matsayin wanda kungiyar Kiristoci za ta mara wa baya bai dace ba.
Shugaban kungiyar Matasan Musulmi da Kiristocin ya fadi haka ne a taron manema labarai a garin Jalingo inda ya ce matsayin na kungiyar Kiristocin ya saba wa halin zaman takewa mai kyau. Kuma zai iya haifar da rashin zaman lafiya a tsakanin mabiya addinai daban-daban da ke jihar.
Mista Garbe Yawe ya ce Jihar Taraba ta kunshi al’ummar Musulmi da Kirista da masu addinin gargajiya, saboda haka wannan ikirari bai dace ba kuma zai iya haifar da zaman gaba a tsakanin mabiya addinan.
Ya ce su matasa mabiya addinan Musulunci da na Kirista sun hada kansu don tabbatar da zaman lafiya a tsakanin al’ummar jihar. Don haka bai kamata a maida wani addini a baya ba domin a siyasance kowane dan kasa yana da damar tsayawa takarar kowane mukami ba tare da la’akari da addini ko kabilansa ba.
Ya kara da cewa don haka ba sa goyon bayan kungiyoyin addinai su tsunduma kansu cikin harkokin siyasa, don haka bai kamata wata kungiyar addini ta fito tana yi wa wani dan siyasa kamfe ba, balle har ta ce ga dan takarar da za a zaba kamar yadda kungiyar CAN reshen jihar ta yi.
Mista Garbey Yawe ya yaba wa wasu bangarori uku na kungiyar CAN da suka ki amincewa da matsayin na kungiyar. Ya ce ya kamata kungiyoyin addinai su guji hada addini da siyasa don kauce wa fada wa rigingimu a lokutan zabe da bayan zabe.
Ana dai zargin cewa fadar Shugaban kasa da ofishin kamfe na Darius Ishaku na ba kungiyar Kiristocin makudan kudi don Kiristoci a jihar su goyi bayan ’yan takarar Jam’iyyar PDP a zabe mai zuwa.