Ya soki masu kiran a kaddamar da yaki gadan-gadan a Arewa maso Gabas

Mataimakin Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar APC a Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Daushe Damagum ya soki yunkurin da wasu ’yan majalisar tarayya ke yi na neman Shugaban kasa ya kaddamar da dokar yaki gadan-gadan a yankin Arewa maso Gabas da ’yan bindiga ke tada kayar baya da zimmar shawo kan lamarin. Alhaji Ibrahim Daushe Damagum ya […]

Ya soki masu kiran a kaddamar da yaki gadan-gadan a Arewa maso Gabas
Ya soki masu kiran a kaddamar da yaki gadan-gadan a Arewa maso Gabas

Mataimakin Sakataren Watsa Labarai na Jam’iyyar APC a Jihar Yobe Alhaji Ibrahim Daushe Damagum ya soki yunkurin da wasu ’yan majalisar tarayya ke yi na neman Shugaban kasa ya kaddamar da dokar yaki gadan-gadan a yankin Arewa maso Gabas da ’yan bindiga ke tada kayar baya da zimmar shawo kan lamarin.
 Alhaji Ibrahim Daushe Damagum ya bayyana haka ne  a tattaunawar da ya yi da Aminiya a Damaturu dangane da cece-kucen da ake yi kan da bayanin da shugaban Majalisar Dattawa ya yi na neman Shugaban kasa ya zartar da yaki gadan-gadan kan ’yan Boko Haram da ke tada kayar baya a jihohin Borno daYobe da Adamawa.
 Ya ce, kowane dan kasar nan ya san yankin Arewa maso Gabas ya shafe sama da shekara biyar cikin halin rikita-rikita amma duk tsawon lokacin da aka dauka ana kashe rayuka da lalata dukiyoyinsu ba  a taba tunanin daukar wannan mataki ba sai a wannan lokaci da aka ga ruwa na kokarin karebwa dan kada ga jam’iyya mai mulkin ta PDP, tare da kokarin dauko salo don kada a gudanar da zabe a jihohin wadanda na Jam’iyyar APC ne.
Ya ce kada a mance a wannan hali ne Jihar Yobe ta gudanar da zaben kananan hukumomi cikin nasara.
Alhaji Ibrahim Damagum ya ce dama sun sa hakan za ta faru ana kewaye-kewaye ne ta hanyar sa dokar ta-baci wadda maimakon ta kawo karshen matsaloli sai kara lalata al’amra take yi.
Ya shawarci ’yan majalisar da ke wakiltar jihohin Yobe da Borno da Adamawa a Majalisar Tarayya su nisanci irin wannan talalabuwa da ake shirin yi wa yankinsu, na a ki gudanar da zabe a jihohinsu, sai daga bisani a shirya zaben da za a yi musu taron dangi domin mamaye jihohin.

KADVS ta daƙile yunƙurin sace yara da ceto wasu a Zariya

Gwamnatin Tinubu na yunƙurin hana ni yin takara — Peter Obi

An gurfanar da ƙarin mutum 17 bisa zarginsu a kisan malama

An kama matashi ɗauke da hannun mutum da bindigogi