Ya tona kabarin mijin mahaifiyarsa ya yanke kansa
Ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa.
Rundunar ’yan sandan Jihar Adamawa ta kama wani mafarauci mai shekara 55, wanda aka fi sani da Gana, kan zargin sa da tona kabari tare da yanke kan mijin mahaifiyarsa.
A cewar jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ’yan sandan, SP Suleiman Yahaya Nguroje, wanda ake zargin ya amsa laifinsa ne a lokacin da ake masa tambayoyi.
- Matashi ya yi lalata da ’yan firamare biyu a Zariya
- Zaftarewar ƙasa ta kashe mata masu haƙar zinare a Mali
Gana wanda ɗan asalin garin Tappare Kona Uku ne a ƙaramar hukumar Jada ta jihar, ya bayyana cewa ɗan marigayin ne ya tuntuɓe shi inda ya buƙaci kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafi bayan rasuwarsa.
Shekara guda bayan binne shi, ɗan ya dawo ya nemi kan mijin mahaifiyarsa don yin tsafin al’adun gargajiya.
Ya yi iƙirarin cewa ɗan mijin mahaifiyarsa ne ya matsa masa lamba, wanda ya yi imanin matsafi ne kuma zai iya cutar da shi ko kuma ‘ya’yansa idan ya ƙi bin umarninsa.
Ya ce, “Na ɗauki fartanya da misalin ƙarfe 4:00 na asubahi, na je maƙabarta, na tona kabari, na yanke kan sa.
Sai ya dawo gida ya ba wa yaron kan a cikin jakar leda.
Wanda ake zargin ya ci gaba da bayanin cewa bayan mako biyu, matar marigayin ta zo wurinsa inda ta shaida masa cewa ta yi munanan mafarki tun lokacin da aka ajiye kan a ɗakin kwanansu.