Ya tsere ya bar matarsa a asibiti bayan ta haifi ’yan uku
Wani magidanci ya gudu ya bar matarsa bayan ta haifi ’yan uku a wani asibiti mai zaman kansa da ke garin Okpoko, Karamar Hukumar Ogbaru a Jihar Anambra. Angon karnin ya yi batar tabo ne saboda ba zai iya biyan dubn N450 da likitoci suka nema kuma tun da ya tafi mako biyu ke nan […]
Wani magidanci ya gudu ya bar matarsa bayan ta haifi ’yan uku a wani asibiti mai zaman kansa da ke garin Okpoko, Karamar Hukumar Ogbaru a Jihar Anambra.
Angon karnin ya yi batar tabo ne saboda ba zai iya biyan dubn N450 da likitoci suka nema kuma tun da ya tafi mako biyu ke nan bai dawo ba.
- EFCC: Kwamitin binciken Magu ya kai wa Buhari rahoto
- An mika wa Masu Zaben Sarkin Zazzau takardar tuhuma
“Kafin na haifi ’yan uku babu abinci a gidan da zamu ci, ina sayar da ruwan leda ne, mijina bai da aikin yi wani lokaci sai ya yi karamin aiki muke samun abin da zamu ci”, inji mai jegon.
Misis Evlyn Odinaka da ke kwance a gadon asibitin da ta haihu ta ce mijinta yana tsammanin samun jariri daya ne kawai.
Sunday Odinaka dan asalin garin Ubaraekwem ne a Karamar Hukumar Ihiala a jihar wanda yake zama da iyalansa a Obodoukwu.
’Yan uku da mai jegon ta haifa sun hada da maza biyu da mace daya kuma kafinsu ta haifi ’ya’ya hudu wadanda a yanzu haka ba sa iya zuwa makaranta saboda iyayen ba sa iya biya musu kudin makaranta.