Ya tuka keke daga Indiya zuwa Sweden saboda soyayya

Wani talaka Ba’indiye da ya damfaru da son wata ’yar masu hali ’yar kasar Sweden, kuma bayan ya aure ta ta koma kasarsu, ya shafe watanni biyar yana tuka keke, inda ya je  kasar da masoyiyarsa take suka hadu.Al’amarin masoyan, ya sanya wadanda suka ji labarin sun dauka tamkar fim din Indiya ne da aka […]

Ya tuka keke daga Indiya zuwa Sweden saboda soyayya
Ya tuka keke daga Indiya zuwa Sweden saboda soyayya

Wani talaka Ba’indiye da ya damfaru da son wata ’yar masu hali ’yar kasar Sweden, kuma bayan ya aure ta ta koma kasarsu, ya shafe watanni biyar yana tuka keke, inda ya je  kasar da masoyiyarsa take suka hadu.
Al’amarin masoyan, ya sanya wadanda suka ji labarin sun dauka tamkar fim din Indiya ne da aka shirya da ake shiryawa a Bollywood.
Labarin masoyan ya tabbatar da cewa, garin masoyi ba ya da nisa. Dokta Kumar Mahanandia (PK) an haife shi ne a 1949, kuma ya fito ne daga zuriyar wani masaki Odisha, kuma daga cikin makaskanciyar kabila da ake kira Dhenkanal, amma Allah Ya yi masa baiwa ta zane-zane. Sai dai iyayensa ba su da kudin daukar nauyin karatunsa, sai ma zagi da wulakanci da yake gani daga ’yan kasarsu saboda kabilar da ya fito daga cikinta. Amma a 1971 sai ya samu shiga Kwalejin Koyon Zane-Zane ta birnin New Delhi a kasar Indiya, inda ya shahara saboda zane-zanensa na mutane masu ban sha’awa.
A 1975, sai wannan budurwa ’yar shekara 19 mai suna Charlotte bon Sledbin, da ke karatu a birnin Landan ta samu labarinsa, sai ta tafi kasar Indiya don ya zana hotonta. Suna haduwa kuwa sai soyayya ta kullu a tsakaninsu;  ta yi matukar sha’awar rashin girman kansa. Daga nan fa sai soyayya ta kullu.
Charlotte har sauya sunanta ta yi zuwa irin na Indiyawa, saboda soyayya har suka yi aure bisa ka’idojin al’adun mutanen Indiya. Sunan Indiyanci da ta lakaba wa kanta kuwa shi ne, Charulata.
Da lokacin tafiyar Charlotte ya yi, sai ta bukaci mijinta ya biyo ta, amma Kumar PK lokacin yana karatu, sai ya ce mata sai ya kammala karatunsa. Sai kuma ta yi masa alkawarin tikitin jirgin sama, amma ya ki, inda ya nuna mata cewa zai zo a kashin kansa. Bayan ta koma gida, sai suka rika yi wa juna wasika.
Da soyayyar Charlotte ta cika zuciyar Kumar sai ya yunkura don cika alkawarinsa, amma a lokacin ba ya da kudi. Duk da haka bai karaya ba. Sai ya sayar da dan abin da ya mallaka, ya sayi kwancen keke, ya daure kayan zanensa, ya fara tafiya.
Wannan masoyi ya fara tafiya zuwa kasar masoyiyarsa a 1978, inda ya ratsa kasashen da suka hada da: Afghanistan da Iran da Turkiyya da Bulgeriya da Yugoslabiya da  Jamus da Austeriya da Denmark. Kekensa ya sha lalacewa a hanya, kuma yakan shafe kwanaki ba ya da abincin da zai ci. Duk haka bai fasa ba, don gudun kada ya karya alkawari. Bayan wata hudu da makonni uku sai ga shi ya isa birnin Gothenburg da ke kasar Sweden
A wancan zamani ba kowace kasa ake bukatar biza ko izin shiga ba.
Hukumomin kasar sai suka tsare shi a wannan wuri, musamman saboda mamakin da suka cika da shi na cewa, ’yar sarauta daga kasar Turai har ta je Indiya ta auri dan talakawa. Jin cewa, ita ’yar sarauta ce, sai Kumar PK ya fara tababa kan ko masoyiyar tasa za ta amince da shi. Sai kawai ta tuko mota ta zo ta tarbi mijinta.
Bayan shekara 40 da aurensu, har sun samu ’ya’ya biyu, wadanda a yanzu suke zaune a kasar Sweden. Mutanen kauyen da a da ke kyarar kabilarsu, tarba ta musamman suka yi wa Dr Kumar PK Mahanandia, domin ya zama jakadan yada al’adun Odiya na kasar Indiya a kasar Sweden.