Ya yaba kan soke bikin kwana 100 na gwamnatin Jihar Jigawa

Sakataren mulki na karamar kukumar Kazaure Malam Jamilu Muhammed Zaki ya yaba wa Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar kan soke bikin cika kwana 100 a gadon mulki.Sakataren ya bayyana haka ne lokacin da yake hira da wakilinmu a farkon wannan mako, inda ya ce ya yaba kan yadda Gwamnan ya ki amincewa da dibar […]

Ya yaba kan soke bikin kwana 100 na gwamnatin Jihar Jigawa
Ya yaba kan soke bikin kwana 100 na gwamnatin Jihar Jigawa

Sakataren mulki na karamar kukumar Kazaure Malam Jamilu Muhammed Zaki ya yaba wa Gwamnan Jihar Alhaji Muhammadu Badaru Abubakar kan soke bikin cika kwana 100 a gadon mulki.
Sakataren ya bayyana haka ne lokacin da yake hira da wakilinmu a farkon wannan mako, inda ya ce ya yaba kan yadda Gwamnan ya ki amincewa da dibar dukiyar jama’a a yi bikin sharholiya da almubazaranci, inda ya ce su ma a nasu bangaren ba za su yi bikin komai ba maimakon haka addu’a za su yi a masallatai domin neman albarka ga gwamnatin.
Malam Jamilu Zaki ya ce babu abin da al’ummar jihar za su ce da Gwamna Badaru sai godiya domin ya toshe duk hanyoyin da barayin gwamnati za su wawure dukiyar jama’a, kuma wannan ne ya sa wasu suke jin haushi suke yawo suna bata gwamnatin jihar.
Ya ce ko ba komai Badaru ya toshe hanyoyin barna da ake yi a jihar an kuma soma gano ma’aikatan bogi da ake amfani da su wajen sace dukiyar gwamnatin jihar, inda ya ce hakan zai taimaka a dauki ma’aikata na gaskiya da suke bukatar aikin yi a gwamnatin jihar.
Jamilu Zaki ya gode wa gwamnatin jihar kan ba da kwangilar gyaran ruwan Kazaure da matsalarta ta ki ci ta ki cinyewa shekaru masu yawa.
Daga ya juya kan majalisar karamar Hukumar Kazaure Sakataren ya ce yanzu haka karamar hukumar ta kafa kwamitin da zai shawo kan matsalar karancin wutar lantarki da jama’ar masarautar Kazaure da dambatta suke fuskanta.
Ya kuma yaba wa dogarawan Hisba kana hana ayyukan badala a yankin tare kira ga jama’ar yankin sub a gwamnatin jihar hadin kai da goyon baya don kai jihar ga tudun mun tsira.