Ya yanke rabin azzakarinsa ya jefar
Wani mai suna Idris Mohammed dan asalin Jamhuriyar Nijar ya yanke rabin azzakarinsa ya jefar a cikin kwata a Jihar Legas.Mutumin wanda a zahiri ba alamar hauka a tare da shi kuma ya ce ba ya shaye-shaye ba ya ga taba, ya shaida wa Aminiya cewa da kansa ya sayo reza ya yanke rabin azzakarin […]

Wani mai suna Idris Mohammed dan asalin Jamhuriyar Nijar ya yanke rabin azzakarinsa ya jefar a cikin kwata a Jihar Legas.
Mutumin wanda a zahiri ba alamar hauka a tare da shi kuma ya ce ba ya shaye-shaye ba ya ga taba, ya shaida wa Aminiya cewa da kansa ya sayo reza ya yanke rabin azzakarin ya jefar.
Ya ce wannan ne karo na biyu da ya ji cewa ya yanki wani bangare na jikinsa, inda ya ce na farko ya ji kamar ya sa wuka ya yanke kansa ta yadda zai mutu, amma sai daga baya ya ji abin ya sake. Ya ce wannan ya faru shekara takwas da suka wuce ne.
Ya ce lokacin da ya yanki kansa bai san abin da yake ciki ba, domin da daddare ne ya yi wa kansa wannan danyen aiki, amma karfe 5:00 na Asuba na yi, sai ya ji ya dawo cikin hankalinsa, a lokacin ne ya fara jin zafi ya shiga kuwwa har mutanen gidan da yake gadi suka ji sai suka kai shi asibiti.
Game da ko ya nemi ’ya ko matar wani ne aka yi masa haka, sai ya ce ba dayan biyu. Kuma ya ce bai taba aure ba, don haka bai san yadda rayuwa za ta kasance masa ko zai iya saduwa da mace ba, sai dai ya ce lokacin da ake yi masa aiki mace ce ta nannade masa azzakarin da bandeji, inda ya ji ta motsa.
Da wakilinmu ya tambayi likitan da ya yi masa tiyata Dokta Oladipo Tola Izik kan ko azzakarin mutumin zai kara amfani, sai ya ce kwarai da gaske kuma zai iya yi wa mace ciki, sai dai a wani lokaci can gaba zai samu matsala, shi ma ana iya yi masa tiyata.
Sarkin Hausawan Idi Araba Alhaji Hassan Auyo wanda wakilinmu ya tarar da mutumin a gidansa, ya ce abin da Idris ya fada shi ya fada masa, ya ce bai shaye-shaye. Sarki Hassan ya ce yana ganin kila aljannu ne suka sa shi aikata wa kansa wannan danyen aiki. Sarkin ya ce za a hada masa kudi domin ya shiga mota ya koma kasarsu Jamhuriyar Nijar.
Idris yana aikin gadi ne a wani gida a unguwar Surulere a Legas, kuma ya ce ya kwashe shekara 10 a gidan, ya ce yanzu yana son ya yi aure.
Wakilinmu ya yi kokarin jin ta bakin mutanen gidan da yake gadi, amma suka ce ba za su yi magana da manema labarai ba.