Ya yi barazanar kashe kansa saboda budurwarsa ta ki aurensa
Wani matashi mai suna Muhammad Naziru Sulaiman, mai kimanin shekaru 26, ya yi barazanar kashe kansa saboda budurwarsa mai suna Rukayya ta ki aurensa.Naziru, dan asalin Jihar Kano da ke sana’ar acaba a unguwar Egbeda a Legas, ya kara yin furucin hakan a yayin da yake tattaunawa ta musamman da Aminiya.Ya ce, “Gaskiya abin da […]

Wani matashi mai suna Muhammad Naziru Sulaiman, mai kimanin shekaru 26, ya yi barazanar kashe kansa saboda budurwarsa mai suna Rukayya ta ki aurensa.
Naziru, dan asalin Jihar Kano da ke sana’ar acaba a unguwar Egbeda a Legas, ya kara yin furucin hakan a yayin da yake tattaunawa ta musamman da Aminiya.
Ya ce, “Gaskiya abin da budurwata Rukayya ta yi mini ne ya sa na yanke shawarar kashe kaina. Rukayya ta yaudare ni, ta ci amanata, saboda ta ki aurena. Duk da soyayyar da nake nuna mata tare da kauna da tausayinta da nake yi, na dauke ta a matsayin kanwata kuma ’yar uwata. Yanzu na shiga wani hali, na rasa yadda zan yi da kaina saboda haka, sai na yanke shawarar na kashe kaina don na huta da bakin cikin da ta sanya ni a ciki”.
Ya bayyana cewa tuni ya shiga damuwa, wacce ta kai har ba ya iya cin abinci saboda bakin cikin da ya shiga na rasa budurwarsa.
Saboda son da yake yi mata ya ce ya sanya hotunanta a jikin babur dinsa na acaba don ya rika tunawa da ita.
Yayin da Aminiya ta tuntube ta, Rukayya ta bayyana cewa ta yanke shawarar yanke hulda da shi saboda ba ta son sa. “Ni da ma can ba na sonsa, shi ne yake ta matsa mini, yake damuna cewa yana sona. Ba ni na ce ina sonsa ba. Ya dade yana bata lokacinsa, kuma ma akwai lokacin da na fito karara na nuna masa cewa ba na sonsa kuma ba na kaunarsa, amma ya ki ji. Shi ne yanzu da na sami miji zan yi aure yake bakin ciki, yake ta sambatu iri-iri, kamar wanda ya tabu”. Inji ta.
Rukayya ta shawarci Naziru kada ya hallaka kansa, ya hakura ya nemi wacce za ta so shi, ba tare da wata matsala ba.
Abokan Naziru sun bayyana cewa ya sha yunkurin kashe kansa suna hana shi, a kan budurwasa.