Ya yi bayan gidan kulli 113 na hodar iblis a filin jirgi

Mutumin ya shafe shekaru 10 a kasar Sifaniya yana safarar migayun kwayoyi.

Ya yi bayan gidan kulli 113 na hodar iblis a filin jirgi

Wani mai safarar miyagun kwayoyi da aka kama ya yi kashin kulli 113 na hodar iblis a filin jirgin sama na Murtala Mohammed da ke Legas.

An cafke mutumin da hodar iblis din da kudinta ya kai Naira miliyan 423 ne a lokacin da ake tantance fasinjojin wani jirgi zuwa birnin Madrid na kasar Sifaniya a ranar bikin Ista.

“Bayan bincikar bayan gidansa na tsawon awa 24, mutumin wanda ya shekara 10 da zama a kasar Sifaniya, ya fitar da kulli 39 na hodar iblis kulli, gaba daya kulli 113 ya fitar a bayan gari biyar da ya yi.

“Bayan bincike, an gano cewa ya tura hodar iblis din ta duburarsa ne a wani otel da ke Igando a Legas, kafin ya je filin jirgin,” inji Kakakin Hukumar Hana Sha da kuma Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) na Kasa, Femi Babafemi.

Ya ambato Kwamandan NDLEA na filin jirin, Ahmadu Garba yana cewa, “Wanda ake zargin ya fitar ta da kulli 39 da nauyinsu ya kai gram 600 da karfe 9.58 na safiyar 5 ga Afrilu; kulli 13 da nauyinsu ya kai gram 200 da karfe 6.30 na yamma; kulli 16 da nauyinsu ya kai gram 250 da karfe 1.30 na dare; washegari, 6 ga Afrilu kuma da da kare 7.30 na safe ya fitar da kulli 32 da nauyinsu ya kai gram 500.”

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya