Ya yi gudun kilomita 600 zuwa gida a kasar Sin

Wani mutumin kasar Sin, mai suna Huang changyong, dan shekara 33, ya ruga zuwa gida, inda ya share kilomita 600 don halarta wasannin sabuwar shekara. A irin wannan lokaci, mafi yawan al’ummar kasar sin da ke zaune a wasu sassan kasa, na garzayawa zuwa garuruwansu na haihuwa, inda sukan yi rububin hawan motocin bas-bas da […]

Ya yi gudun kilomita 600 zuwa gida a kasar Sin
Ya yi gudun kilomita 600 zuwa gida a kasar Sin

Wani mutumin kasar Sin, mai suna Huang changyong, dan shekara 33, ya ruga zuwa gida, inda ya share kilomita 600 don halarta wasannin sabuwar shekara. A irin wannan lokaci, mafi yawan al’ummar kasar sin da ke zaune a wasu sassan kasa, na garzayawa zuwa garuruwansu na haihuwa, inda sukan yi rububin hawan motocin bas-bas da kananan motocin hawa da Babura. Shi kuwa wannan matashi sai ya aikata sabanin yadda mutane suka saba yin tafiya mai nisa a wannan zamanin.
Huang dai tuni ya tsara yadda zai shafe kwana tara yana gudu har zuwa gidan su, da ke birnin Shenzhen, a kudancin kasar Sin da ke Lardin Guangdong a garin Chengzhou da ke tsakiyar kasar Sin a gundumar Hunan.
A tsarin gudun wannan matashi, ya shirya yadda zai rika share kilomita 70 a kowace rana, har ya cimma adadin tafiyarsa zuwa na tsawon kilo0mita 600.
Wannan matashi ya isa garin su a yau Juma, 29 ga watan Janairun bana. Dama shi dan wasan gudu, wanda ya shafe shekara 18 yana tsere. Kuma a lokacin da yake yin wannan gudun, mutane da dama sai tsayar da shi suke yi don su dauki hoto tare da shi. Ya ce, ya kara samun kwarin gwiwa a wannan tseren da ya yi zuwa gida, a daidai lokacin da ya gane cewa yana ta kusantowa zuwa gida.