Ya yi karar dansa akan aure daga makaskancin jinsi

Wani uba a kasar Indiya ya kai karar dansa, inda ya bukaci ya biya shi diyyar kudin Indiya rupees miliyan 10, saboda ya bata masa suna, a dalilin auren da ya yi daga makaskancin jinsin kasar.Sidhnath Sharma, ya bukaci dansa Sushant Jasu ya daina amfani da sunan zuri’arsu. Kotun da ya kai kara a Jihar […]

Ya yi karar dansa akan aure daga makaskancin jinsi
Ya yi karar dansa akan aure daga makaskancin jinsi

Wani uba a kasar Indiya ya kai karar dansa, inda ya bukaci ya biya shi diyyar kudin Indiya rupees miliyan 10, saboda ya bata masa suna, a dalilin auren da ya yi daga makaskancin jinsin kasar.
Sidhnath Sharma, ya bukaci dansa Sushant Jasu ya daina amfani da sunan zuri’arsu. Kotun da ya kai kara a Jihar Bihar ta shirya sauraren karar a karshen wannan makon.
Lauyan da yake kare mai kara, Sharma, kuma dan kabilar madaukaka a cikin al’ummar Bhumihar, ya bayyana cewa wannan auren da aka yi a bara, ya keta al’adar da suka shafe shekara 400 suna gudanar da ita.
“Tsawon shekaru muna gudanar da auratayya ne a tsakaninmu,” a cewar Sharma, kamar yadda ya bayyana wa Kamfanin Dillancin Labarai na AFP, a hirar da aka yi da shi a garinsu na Danapur, da ke wajen babban birnin Patna.
“Sai dai lokacin da dana daya tilo ya karya wannan al’ada, baya ga damuwar da na shiga, ya kuma kaskantar da kimata a cikin al’umma. Ba zan taba mantawa ba, ba kuma zafe masa ba,” inji shi.
Ita kuwa mahaifiyar Jasu, wadda ta bukaci a sakaya sunanta, ta ce matukar danta yana cike da farin ciki a aurensa, za ta goya masa baya. Shi ma Jasu ya ki cewa uffan.
Gwamnatin Jihar Bihar ta bullo da shirin karya lagon wannan al’ada, inda a bara ta rika bai wa matan da suka yi aure a wajen rukuninsu tallafin rupees dubu 50.

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda

‘Yan bindiga sun ƙone gidan mai da motoci 4 a Enugu

Kwalara ta kashe fiye da mutum 300 a Sudan