Ya yi karar matarsa kan haifa masa munanan ’ya’ya
Wani mutumin kasar Sin Jian feng ya yi karar matarsa saboda Haifa masa munanan ’ya’ya, kamar yadda jaridar Irish Times ta ruwaito. “Na auri matata saboda soyayya, amma lokacin da ta fara haihuwar ’ya ta farko sai muka fara samun matsala da ita,” kamar yadda ya bayyana wa Irish Times. “’Yarmu ta yi matukar muni, […]
Wani mutumin kasar Sin Jian feng ya yi karar matarsa saboda Haifa masa munanan ’ya’ya, kamar yadda jaridar Irish Times ta ruwaito. |
“Na auri matata saboda soyayya, amma lokacin da ta fara haihuwar ’ya ta farko sai muka fara samun matsala da ita,” kamar yadda ya bayyana wa Irish Times. “’Yarmu ta yi matukar muni, har ta kai ga tana ba ni tsoro,” inji shi.
Da farko Jian ya zargi matarsa da lalata a waje, saboda yana da tabbacin cewa babu yadda za a yi ya zama uba ga mummunan da. Sai dai da aka gudanar da gwajin kwayoyin halitta sai aka tabbatar masa cewa nasa ne. Da aka wanke matarsa daga zargi, sai ta fito ta bayyana masa gaskiya cewa, an yi mata kwaskwarimar gyaran siffa, inda ta kashe Dala dubu 100 wajen aikin a kasar Koriya ta Kudu kafin haduwarsu.
Feng ya yi karar matarsa kan yaudararsa da ta yi, ta hanyar kin bayyana masa gaskiyar yadda aka gyara mata siffa ta zama kyakkyawa, har ta kai ga damfararsa ya dauka ita kyakkyawa ce. Alkali ya amince da hujjar Feng, don haka ya bayar da umarnin matar ta biya shi Dala dubu 120.