Ya yi karyar ya mutu don ya cinye bashin Naira miliyan 223

Staveley zai shafe shekara hudu da rabi a gidan yari.

Ya yi karyar ya mutu don ya cinye bashin Naira miliyan 223

David Staveley

An yanke wa wani mutumin Jihar Massachusetts da ke Amurka hukuncin dauri bayan ya yi yunkurin yin zamba a karkashin shirin tallafin kasuwanci na COVID-19.

Mutumin ya yi karyar cewa ya mutu don guje wa hukumomin kasar kan tallafin bashin da aka ba shi. An dai yanke masa hukuncin daurin wata 56 ne a gidan yari.

Wanda ya aikata laifin mai suna David Staveley ya yi ikirarin cewa, ya mallaki manyan kamfanoni hudu inda ya bukaci Dala dubu 544,(kimanin Naira miliyan 223 da dubu 350) a matsayin tallafi daga gwamnatin kasar.

Bayan da aka tuhume shi a bara, Staveley ya yi karyar ya mutu kuma ya yi amfani da bayanan karya ta hanyar satar lasisin lambar mota.

Shi ne mutum na farko da aka tuhume shi da laifin zamba kuma yana bukatar tallafi.

Masu gabatar da kara sun yi Allah- wadai da matakin nasa a cikin sanarwar yanke hukuncin.

“Ya yi tunanin amfani da matsalar tattalin arziki da cutar ta haifar a matsayin wata dama ta wadata kansa ta hanyar amfani da damar aka ware wa mabukata.”

Staveley mai shekara 54, da abokin aikinsa, David Andrew Butziger mai shekara 53, sun shirya bayanan karya a matsayin masu gidajen abinci guda uku da kasuwancin da ba a aiwatar ba mai suna Dock Wireless, duk da suna da “manyan albashi kowane wata.”

A cewar Ma’aikatar Shari’a, “Wani dan kasa da ya damu da yanayin yaudararsu” ya fallasa su don a yi bincike a kan lamarin.

An kama mutanen biyu a watan Mayun bara, kuma an mika Staveley zuwa gidan yari bayan an tuhume shi.

Makonni bayan haka, ya yanke na’urar sa-ido a kan na’urar lantarkinsa, inda ya bar bayanan da suke nuna ya kashe kansa tare da abokansa da ’yan uwansa, sannan ya ajiye motarsa da ba a bude ba a bakin teku, kamar yadda sashen shari’a na jihar ya bayyana.

Staveley zai shafe shekara hudu da rabi a gidan yari, sai kuma shekara uku na gyaran hali bayan ya gama zaman gidan yarin.

Mista Butziger ya amsa laifin da ake zarginsa na hada baki wajen aikata zamba a banki.

Za a yanke masa hukunci a cikin wannan wata na Nuwamba.