Ya yi mutuwar ƙarya don ƙin biyan kuɗin makarantar ɗansa

Kotu ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari, da kuma tarar Dala 500,000.

Ya yi mutuwar ƙarya don ƙin biyan kuɗin makarantar ɗansa

Wani mai shekaru 39 a Jihar Kentucky ta Amurka, Jesse Kipf, na fuskantar hukuncin ɗaurin shekara bakwai saboda shiga tsarin rajistar matattu ta Intanet ba bisa ƙa’ida ba, da kuma yin ƙaryar mutuwarsa don ƙin biyan Dala dubu 100 na kuɗin karatun ɗansa da tsohuwar matarsa ta haifa.

Jesse ya amince ya shiga rajistar sunayen matattu a Hawaii ta hanyar amfani da bayanan shiga tsarin wanda ya sace daga wajen wani likita a jihar a watan Janairun bara.

A cewar masu bincike, ya ƙirƙiro kuma ya sanya wa kansa fayil a cikin tsarin kuma ya kwaikwayi likitan don tabbatar da cewa ya mutu.

Takardun   kotu sun nuna cewa Jesse ya amince da shiga shafukan Intanet daban-daban a jihohin Arizona da Ɓermont ke gudanarwa ba bisa ƙa’ida ba, tare da Kamfanin GuestTek  Interactive

Entertainment  and Milestone, Inc., wanda ya kai ga lissafa shi a cikin waɗanda suka mutu a kundin bayanan matattu na gwamnati.

A wata yarjejeniya da aka yi, wanda ake zargin ya yi iƙirarin cewa ya aikata waɗannan laifuffuka ne, a wani ɓangare don kauce wa biyan bashin kuɗaɗen makarantar ɗansa.

“Ya kammala cike takardar shaidar mutuwa ta Jihar Hawaii, sannan, a ranar 21 ga Janairu, 2023, wanda ake tuhumar ya sanya kansa a matsayin mai ba da takardar shaidar likita game da shari’ar kuma ya ba da shaida,” in ji takardar hukuncin.

“Ya sanya hannu a madadin likitan ta Intanet, ya ba da sunansa da takensa da lambar lasisi. Wannan ya sa aka yi wa wanda ake tuhumar rajista a matsayin wanda ya rasu a yawancin kundayen bayanan gwamnati.”

Ƙarin munin abin, Jesse ya amince da yin kutse a cikin harkokin kasuwanci masu zaman kansu da na gwamnati da na kamfanoni ta hanyar amfani da takardun shaidar da aka sace daga wasu mutane, kuma ya yi ƙoƙarin sayar da hanyoyin shiga tsarin sadarwa ga masu saye ta Intanet.

A ranar 29 ga Maris, 2024, Jesse ya amsa laifinsa na zamba ta amfani da kwamfuta da kuma laifin satar bayanan sirri.

Bisa  takardar yarjejeniya, Jesse dole ne ya biya waɗanda ya zambata Dala 116,000 (kimanin Naira miliyan 148 da dubu 712 da tallafawa da Dala 79,000 (kimanin Naira miliyan 101 da dubu 278 ga gwamnati da cibiyoyin sadarwar da ya shiga ba bisa ƙa’ida ba.

Duk da haka, shari’ar ta yanke masa hukuncin ɗaurin shekara bakwai a gidan yari, da kuma tarar Dala 500,000, (kimanin Naira miliyan 641 da dubu 100).

Tinubu ya yi naɗin sabbin muƙamai huɗu

Majalisar Zartarwa ta amince da kusan Naira tiriliyan 50 Kasafin Kuɗin 2025

Tinubu ya jagoranci zaman Majalisar Zartarwa

HOTUNA: Ana shirye-shiryen jana’izar marigayi Lagbaja