Ya yi sata awanni da zuwa neman aiki a kamfanin da ya je
Wani da yake fatar zama ma’aikacin wani kamfani ya yi gaggawa wajen bayyana rashin gaskiyarsa bayan ya yi nazarin farashin wani daga cikin hajar kamfanin. Mai neman aikin dan Jihar Wyoming da ke yammacin qasar Amurka, an kama shi bisa zargin satar ne bayan ya wallafa farashin wasu kayan motsa jiki da ya sato ciki […]
Wani da yake fatar zama ma’aikacin wani kamfani ya yi gaggawa wajen bayyana rashin gaskiyarsa bayan ya yi nazarin farashin wani daga cikin hajar kamfanin.
Mai neman aikin dan Jihar Wyoming da ke yammacin qasar Amurka, an kama shi bisa zargin satar ne bayan ya wallafa farashin wasu kayan motsa jiki da ya sato ciki har da tabarau da harsashi a matsayin kayan sayarwa. Ya yi haka ne kafin ya mayar da takardar neman aikin da ya karbo a wajen masu daukarsa aiki.
A makonnin da suka gabata ne, ’yan sandan Gillete suka sanar da cewa, an sace wani tabarau da kudinsa ya kai Dalar Amurka 90 (kimanin Naira dubu 28) da kuma harsasan bindiga 30-30 da kudinsu ya kai Dala 49.98. ’Yan sandan sun bayyana wanda ake zargin da matashi mai shekara 36, kuma yana amfani da katin saye da sayarwa wajen sayen wasu abubuwa, kamar yadda wani faifan bidiyo ya nuna kuma kafar labarai ta Gillette News, ta ruwaito.
Jami’an tsaron sun gurfanar da mutumin wanda aka sakaya sunansa a gaban kotu, inda ake tuhumarsa da sata sannan an gano wasu abubuwa da suka bace a hannunsa. Bayan binciken da aka gudanar an tabbatar da yana da masaniya kan abubuwan da suka bace.