Ya yi sata don a tsare shi ya rika samun abinci a bagas
Ya dage lallai sai an kira ’yan sanda a kama shi.
Wani mai shekara 60 ya girgiza mazauna wani tsibiri a kasar Thailand bayan ya yi sata a wani kantin magani don a kama shi a kai shi gidan yari saboda yana fama da tsananin talaucin da ba zai iya daukar nauyin kansa ba.
Lamarin da ba a saba gani ba, ya faru ne a yammacin ranar 29 ga Yulin bana, a wani kantin magani da ke Lardin Chonburi, Kudu da Bangkok Babban Birnin Kasar.
- Yadda gobarar daji da fari ke neman durkusar da kasashen Turai
- Mutum 16 sun mutu, 21 sun jikkata a hatsarin mota a Turkiyya
Mutumin wanda daga baya ’yan sanda suka bayyana sunansa da Phichit, an kama shi ne yana satar sandunan sabulu uku da kudinsu ya kai kudin kasar Thai Bath 17, (kimanin Senti 47 na Dalar Amurka daidai da Naira 196.87), inda ma’aikatan kantin suka kama shi.
Cikin kantin a fayyace yake wajen fadakar da masu sayayya game da yin sata a kantin, inda masu laifi ke fuskantar yi masu tarar ninki 30 na kudin kayan da suka sata da karin dauri a kurkuku.
Sai dai ma’aikatan kantin sun yarda su bar wannan tsoho ba tare da ya fuskanci hukunci ba.
Wani ma’aikacin kantin ya ba da shawarar ya biya tarar kudi. Amma ba a same shi da kudi ba, inda ya dage cewa ma’aikatan su kira ’yan sanda a kama shi.
Phichit ya bukaci a kama shi saboda laifin da ya aikata, don haka ma’aikatan kantin ba su da wani zabi illa kiran ’yan sanda.
A lokacin da ake masa tambayoyi, ya ce ya fi son ya dauki lokaci a gidan yari, inda zai rika samun abinci sau uku a rana kuma ya rika cudanya da sauran mutane, maimakon yawo a kan titi ba tare da aikin yi ba da kuma hadarin kamuwa da yunwa wacce ka iya sanadin mutuwarsa.
Ba a dai san yadda ’yan sanda suka zabi shawo kan lamarin ba, amma labarin Phichit yana nuna munin halin da jama’ar Thailand da dama ke ciki a yanzu, inda hauhawar farashin kaya ya kai mataki mafi girma tun shekarar 2008.
Wannan mutum mai shekara 60 ba shi ne mutum na farko da ke neman a kama shi da gangan ba.
A shekarun baya, an samu rahoton wani Ba’amurke da ya yi kokarin yin fashi a banki don kawai a kama shi ya yi nesa da matarsa da take sa shi bakin ciki.
Sai kuma mutumin da ya yi fashi a banki jim kadan bayan kammala daurin shekara 20 a gidan yari, saboda bai saba da rayuwa a waje ba.