Ya yi wa dansa kyautar benen gidan katako don aurensa
Wani kafintaa birnin Shaandi da ke kasar Sin ya gina wa dansa gida mai hawa biyu na katako, a matsayin kyautarsa ta aure. Ya yi wannan ginin ne shi kadaui da hannunsa.Zheng Zhongfu dan shekara 54, kafinta ne da ke zaune a kauyen Hudian da ke Arewa maso Yammacin kasar Sin, da ke karkashin Lardin […]
Wani kafintaa birnin Shaandi da ke kasar Sin ya gina wa dansa gida mai hawa biyu na katako, a matsayin kyautarsa ta aure. Ya yi wannan ginin ne shi kadaui da hannunsa.
Zheng Zhongfu dan shekara 54, kafinta ne da ke zaune a kauyen Hudian da ke Arewa maso Yammacin kasar Sin, da ke karkashin Lardin shaandi. Ya kuma fara koyon aikin kafint ane a wurin mahaifinsa tun yana dan shekara 17, inda kwarewarsa a wannan sana’ar ta sanya yake tunanin kera wasu abubuwa da daban. A lokacin da ya ga dimbin mace-macen da aka yi sanadiyyar girgizar kasa, sai ya yi tunanin cewa, a rika yin gini da kayana aikin da ba su da nauyi.
Zheng ya fara tattara bayanai daga shafukan intanet kan yadda ake kera gidan katako, tare da taimakon dansa. Ya fara fito da zayyana gidan katako a shekara ta 2012. Bayan shekara hudu yana yin ’yan gyare-gyare a kan zayyanar sai ya fara gina gidan cikin wannan shekarar.
Ana sa ran kammala wannan gidan katako mai hawa biyu, da ke da fadin murabba’in mita 300. Ganin cewa karamin dansa na shirin yin aure nan da Oktoba, ya yi niyyar bayar da gidan a matsayin kyautar aure. Ita ma amaryar dansa ta zaku da farin cikin ganin ta tare a gidan.
Sai dai wani abin takaici, kwararrun masana zayyanar gine-gine, sun nuna tababar su game da nagartar katako a wajen gini. Kodayake katako na da kyau wajen bayar da kariya ga rana da kyautata muhalli, abin damuwar shi ne rufin gidan, wanda kirare ne da ka iya cin wuta, ko kuma a girgide su cikin sauki.