Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari
Ibrahim Yucel ya shafe shekaru 26 yana shan taba kuma duk da yunƙurin dainawa, ya kasa daina zukar fakiti biyu a rana.
![Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari Ya yi wa kansa keji don daina shan sigari](https://aminiya.ng/wp-content/uploads/2025/02/images-7.jpeg)
Ibrahim Yucel ya shafe shekaru 20 yana zukar taba sosai a lokacin da ya yanke shawarar ci gaba da zuka sosai.
Jarabar son kowane irin abu ba shi da kyau, kuma zukar taba tana cikin mafi muni.
- Amurka ta dakatar da bai wa Afirka ta Kudu tallafi
- Yadda rikicin shugabanci ya janyo rufe babban masallacin gari
Barin shan taba yana da matukar wahala, yana bukatar jajircewa da sadaukarwa.
Duk da gagarumin kokarin da suke yi, kadan ne kawai na masu zukar sigari suka sami nasarar shawo kan jarabar son da suke yi mata.
Kimanin shekara 11 da suka gabata, labarin wani mutum na kokarin daina shan taba ya shahara a talabijin da sauran kafafen yada labarai lokacin da ya saka keji a fuskarsa don ya daina zukar taba.
Mutumin dan kasar Turkiyya mai suna Ibrahim Yucel ya saka keji a kansa ne mai kamar hular karfe mai siffar kwallo domin ya daina zukar taba.
A cikin 2013, jaridu sun ba da rahoton cewa, Ibrahim Yucel ya shafe shekaru 26 yana shan taba kuma duk da yunƙurin dainawa, ya kasa daina zukar fakiti biyu a rana.
A duk shekara, a zagayowar ranar haihuwar ’ya’yansa uku da ranar aurensa, sai ya daina zukar sigari, amma bai wuce kwanaki ba, sai ya koma ruwa.
Duk da cewa, hotuna da bidiyo na yadda ya kulle kansa a keji yana bai wa matarsa mabudin budewa ya yi shuhura, har yanzu babu wata kwakkwarar shaida da ke nuna ya daina zukar tabar.
A cewar Hukumar Lafiya ta Duniya, a duk shekara, sama da mutane miliyan 8 ne ke mutuwa sakamakon shan taba.
Galibin mace-macen da ke da alaka da taba sigari na faruwa ne a kasashe masu karamin karfi da matsakaita, wadanda galibi ake tallace-tallace a masana’antar taba.
Taba kuma tana iya zama mai kisa ga masu zukar ta.
Haɗarin hayaki a wani ɓangare na biyu kuma yana da mummunan tasiri a kan lafiya, inda yake haifar da mutuwar mutane miliyan 1.2 a shekara.