Ya yi wa ’yar bautar kasa fyade kuma ya kashe ta
Al’ummar garin Abekuta sun wayi gari da abin alhini, yadda wani mutum mai suna Festus Udoh ya yaudari wata mai yi wa ƙasa hidima, ya yi mata fyaɗe kafin daga bisani ya kashe ta. Matar ’yar hidimar ƙasa hidima mai suna Modupe Taiyese, ’yar kimanin shekara 23, tana koyon tuƙin mota ne a wata makaranta, […]
Al’ummar garin Abekuta sun wayi gari da abin alhini, yadda wani mutum mai suna Festus Udoh ya yaudari wata mai yi wa ƙasa hidima, ya yi mata fyaɗe kafin daga bisani ya kashe ta.
Matar ’yar hidimar ƙasa hidima mai suna Modupe Taiyese, ’yar kimanin shekara 23, tana koyon tuƙin mota ne a wata makaranta, inda mutumin da ake zargi ke aiki.
Kwaminshinan ’yan sanda a Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya shaida wa Aminiya cewa jami’in da ke kula da masu hidimar ƙasa a Abekuta ne ya sanar masu cewa ɗaya daga cikin ’yan hidimar ƙasa ta yi ɓatan dabo.
“Daga nan sai muka zurfafa bincike, inda muka bibiyi waɗanda ta yi mu’amalar ƙarshe da su, muka kuma gano cewa ta yi maganar ƙarshe ta waya ne da wanda ake zargin.
“Nan muka yi amfani da na’urorin zamani da kimiyya da fasaha muka gano wanda ake zargin. Bayan mun kamo shi, muka yi bincike sai ya nuna mana inda ya je ya yi mata fyaɗe sannan ya kashe ta saboda ta shaida masa cewa za ta sanar wa ’yan uwanta abin da ya yi mata, shi ne ya kashe ta don kar ta tona masa asiri amma cikin ikon Allah yanzu ya shiga hannu, ya kuma amsa laifin sa.
“Sannan lokacin da ya nuna mana inda ya kashe ta bayan kwana uku da abkuwar lamarin, mun iske gawarta har ta fara ruɓa, sannan mun ga ƙananan hotonsa da ya zubar a wajen. Don haka da zarar mun kammala bincike za mu kai shi kotu bisa tuhumarsa a kan laifin fyaɗe da kisan kai,” inji Kwamishina Ahmad Iliyasu.
Haka kuma ya yi kira ga jama’a da su riƙa kiyayewa da irin mutanen da suke ta’ammali da su.
Wakilinmu ya zanta da wanda ake zargin, wanda ya shaida cewa aikin shaiɗan ne ya sa har ya kai ga aikata laifin. Ya ce tuni matarsa ta gudu ta bar shi, bayan saɓanin da suka samu. “A ranar da abin ya faru sai na ji ina son saduwa da mace. To, daman na san marigayiyar kimanin watanni biyu da suka shuɗe, domin tana koyan tuƙi a makarantar koyar da tuƙi da nake aiki amma ba ta zo makarantar ba kimanin makwanni biyu. Sai na kira ta a wayar salula na ce ta zo ta ƙarɓi takardar tuƙinta ta kammala. Ta zo ta same ni a unguwar da nake zaune Lafenwa, daga nan muka hau babur zuwa Iberokodu. Daga nan muka tafi a ƙafa har wurin da lamarin ya faru. Da muka isa jejin na nuna mata buƙatata ta saduwa da ita, sai ta ƙi yarda. Nan na tursasa ta, na sadu da ita. Bayan na gama sai ta ce za ta faɗa wa ’yan uwanta. Shi ya sa na yaga rigarta, na shaƙe ta da ita. Da na ga numfashinta ya fara ɗaukewa sai na gudu na bar ta,” inji Festus Udoh.
Ya ce ya daɗe yana so su ƙulla alaƙar soyayya da ita amma ta ƙi amincewa. “Kafin wannan rana babu wata alaƙar soyayya a tsakaninmu, domin ta ƙi amincewa da ni sai dai kawai muna yin waya da ita,” inji shi.