Ya yi yunkurin halaka kansa akan matarsa ta nemi saki

Wani magidanci mai kimanin shekara 29 ya yi yunkurin halaka kansa lokacin da matarsa ta nemi ya sake ta saboda gazawarsa wajen daukar nauyin iyalinsa.Magidancin mai suna Abdulfatah Abdussalam mazaunin unguwar dorayi a birnin Kano, an gurfanar da shi ne a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Lamba 7 a Sabon Garin Kano. Mai unguwar […]

Ya yi yunkurin halaka kansa akan matarsa ta nemi saki
Ya yi yunkurin halaka kansa akan matarsa ta nemi saki

Wani magidanci mai kimanin shekara 29 ya yi yunkurin halaka kansa lokacin da matarsa ta nemi ya sake ta saboda gazawarsa wajen daukar nauyin iyalinsa.
Magidancin mai suna Abdulfatah Abdussalam mazaunin unguwar dorayi a birnin Kano, an gurfanar da shi ne a gaban Kotun Shari’ar Musulunci da ke Lamba 7 a Sabon Garin Kano.
Mai unguwar dorayi ne ya yi karar Abdulfatah a wurin ’yan sanda a ranar 30 ga Agustan da ya gabata a daidai lokacin da yake yunkurin rataye kansa.
Mai gabatar da kara a gaban kotun ya ce “Kai Abdulfatah Abdussalam ’yan sanda sun kama ka ne a daidai lokacin da kake yunkurin halaka kanka. Wanda hakan laifi ne da ya saba wa sashi na 119 na kundin tsarin shari’a na final kod.”
Wanda ake zargin ya amsa laifinsa, sai dai ya shaida wa kotu cewa ya yi haka ne don ya samu hutu a rayuwarsa saboda tsabar talaucin da yake ciki da kuma matsawar da matarsa take ta yi kan sai ya sake ta.
Mai shari’a Abdu Abdullahi Waiya ya dage shari’ar zuwa ranar 30 ga Satumba tare da bayar da umarnin a tsare wanda ake zargin a gidan kurkuku zuwa ranar da za a sake sauraron karar.