Ya yi yunkurin kona tsohuwar matarsa da mijinta
An gurfanar da wani mutun mai suna Salisu Manu na kauyen Dage da ke cikin karamar Hukumar Dutsi a Jihar Katsina a gaban babbar kotun Majestare ta biyu da ke cikin garin Katsina bisa zarginsa da haddasa gobara tare da yunkurin kisan wasu mutane biyu miji da mata. Kamar yadda dan sanda mai gabatar da […]

An gurfanar da wani mutun mai suna Salisu Manu na kauyen Dage da ke cikin karamar Hukumar Dutsi a Jihar Katsina a gaban babbar kotun Majestare ta biyu da ke cikin garin Katsina bisa zarginsa da haddasa gobara tare da yunkurin kisan wasu mutane biyu miji da mata.
Kamar yadda dan sanda mai gabatar da kara, Sufeto Isa Liti ya shaida wa kotu, karkashin jagorancin mai shari’a Abdu Ladan; wani mutun mai suna Isa Umar na kauyen Raba da ke cikin karamar Hukumar Dutsi ya yi koken cewa suna kwance a daki tare da matarsa a tsakiyar dare, aka kunna wa dakin da suke ciki wuta a lokacin da suke barci. A binciken da ’yan sanda suka gudanar, sun gano cewa wanda ake zargin na da alaka da tashin gobarar, domin shi ne tsohon mijin matar da Isa ke aure a yanzu.
Kamar yadda wata majiya ta shaida wa Aminiya, ana zargin shi Salisu ne ya tafi har gidan Isa da ke can kauyen Raba, ya sanya wa gidan wuta saboda kishin ya auri matar da ya saki. Majiyar ta ce Salisu bai musanta abin da jama’ar da suka kai dauki a wajen kashe gobarar suke cewa ya aikata ba. Sai dai Isa da matarsa sun tsira ba tare da sun ji wani rauni ba.
dan sanda mai gabatar da kara ya ce laifin da ake zargin Salisu da aikatawa ya saba wa sashi na 337 na kundin laifuffuka da hukunce-hukuncensu na Finalkod. Sai dai kuma Mai shari’a Abdu Ladan ya ce,ba zai tuhumi wanda ake zargin ba saboda kotunsa ba ta da wannan hurumin sai babbar kotu. Ya kuma sanya ranar sake ambaton karar zuwa 31 ga watan Janairun badi. Ya bayar da umarnin tura wanda ake zargin zuwa gidan maza.