Ya yi yunkurin kone layin tsohuwar budurwarsa
Wani matashi da so ya rufe wa ido ya yi yunkurin kone layin tsohuwar budurwarsa a unguwar Bachirawa da ke karamar Hukumar Dala a Jihar Kano, sai dai kuma jama’a sun kashe wutar wadda ta takaita a garejin gyaran mota na wani bawan Allah.Matashin mai kimanin shekara 23, mai suna Auwalu Malam ana zargin ya […]

Wani matashi da so ya rufe wa ido ya yi yunkurin kone layin tsohuwar budurwarsa a unguwar Bachirawa da ke karamar Hukumar Dala a Jihar Kano, sai dai kuma jama’a sun kashe wutar wadda ta takaita a garejin gyaran mota na wani bawan Allah.
Matashin mai kimanin shekara 23, mai suna Auwalu Malam ana zargin ya yi wannan aika-aika ne yayin da ya fahimci cewa yarinyar da yake mutuwar so mai suna Zainab ta yi watsi da shi ta kuma maye gurbinsa da wani.
Rahotanni sun ce matashin ya yi barazanar zai kone layin gidan budurwar tasa idan har aka hana shi aurenta. Kuma bayan kwanaki da aurar da ita ga wani, sai ya cinna wuta a layin gidan tsohuwar budurwar tasa inda wani garejin gyaran mota da ke tsakiyar unguwar ya kama da wuta motocin da suke ciki suka kone ciki har da motar Hukumar Hisba.
Aminiya ta tattauna da matashin a Hukumar Hisba inda ya ce, “Har yanzu ina kaunar budurwata, kuma ban san yadda aka yi na aikata abin da ake zargina ba. Saboda haka ba zan yarda da laifin da ake zargin cewa ni na sanya wutar ba.”
Mai garejin motocin da aka kone mai suna Usman Abdullahi ya shaida wa Aminiya cewa bayan matashin ya sa wuta a garejin da muke aiki, sai ya yi barazanar zai kone dukkan gidajen da ke layin a Bachirawa. “Ba na nan lokacin da abin ya faru wani yarona ne ya kira ni ya gaya min cewa matashin ya kone garejinmu. Kuma ya yi yunkurin kone gidajen da ke layin. Jin haka ban yi wata-wata ba na sanar da Hukumar Hisba ba wai don lamarin ya hada da motarsu ba, domin su bi kadin lamarin a bi wa sauran mutane hakkinsu,” inji shi.
Mataimakin Kwamandan Hisba na karamar hukumar Malam Abubakar Mati Salihu ya bayyana wa Aminiya cewa matashin ya sanya wa wutar ne saboda tunanin cewa ’yan unguwar ne suka hada baki aka hana shi aurenta.
Malam Mati Salihu ya kara da cewa “Hukumar Hisba za ta gurfanar da shi a gaban kotu saboda daukar doka da ya yi a hannunsa na yunkuri sanya wuta a gidajen jama’a. Kuma zai fuskanci hukuncin kone mana mota wacce ita kadai muka mallaka da sauran motocin da ya kone a garejin.”