Ya yi yunkurin lalata da kanwar matarsa
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wani magidanci bisa zarginsa da yunkurin yin lalata da kanwar matarsa. Bayanai sun ce an cafke magidancin ne mai suna Nazifi Aminu a lokacin da yake kokarin daukar kanwar matar tasa wacce ita ma matar aure ce zuwa wani wuri don aikata muguwar manufarsa.Matar da ya dauka din […]
Hukumar Hisba ta Jihar Kano ta kama wani magidanci bisa zarginsa da yunkurin yin lalata da kanwar matarsa. Bayanai sun ce an cafke magidancin ne mai suna Nazifi Aminu a lokacin da yake kokarin daukar kanwar matar tasa wacce ita ma matar aure ce zuwa wani wuri don aikata muguwar manufarsa.
Matar da ya dauka din mai suna Zahra’u Sani ta shaida wa Aminiya cewa a wani lokaci mijin yayarta tata ya zo har gidanta inda ya same ta ya fara yi mata maganganun da ba su kamata ba, har ya yi alkawarin daukarta zuwa wani wuri daban. “Wata rana ya zo ya same ni a gida yake gaya min cewa wai me ke damuna duk na rame, na gaya masa ba ni da wata matsala a gidan aurena. Sai ya ce wai na matso kusa zai yi min rada da ya ga na ki sai ya ba ni Naira dubu daya tare da alkawarin cewa zai zo jibi don mu tafi wani wuri,” Inji ta.
Malama Zahra’u ta ce, “Da maigidana ya dawo sai na gaya masa abin da ake ciki, don haka aka shirya masa tarko. Ranar da zai zo sai maigidana da wasu jama’a suka buya a gefen makabratar da muka yi za mu hadu da shi. Ina tsaye sai ga shi a cikin Adaidiata Sahu ya ce yi sauri ki shigo mu tafi. Daga nan jama’ar da ke wurin suka fito suka kama shi aka kawo mu Hukumar Hisba.”
Sai dai Nazifi Aminu ya musanta abin da ake zarginsa, inda ya ce ba wani abu ya sa shi zuwa wurin kanwar matar tasa ba sai don ya taimaka mata. Ya ce ta gaya masa cewa tana cikin matsalar bashi ne, shi ya sa yake kokarin taimaka mata.
Sai dai mahaifin matan biyu, Malam Sani ya nemi wanda ake zargin ya sakar masa ’yarsa saboda bai yarda da dabi’un surukin nasa ba.
Mataimakin Kwamandan Hisba na yankin Dala, Abubakar Mati Salihu, ya tabbatar da faruwar lamarin inda ya ce wanda ake zargin ya saki matarsa kamar yadda mahaifinta ya nema. “Kuma ganin bai aikata masha’ar ba, ya sa muka sallame shi. Mun yi masa nasihohi tare da neman ya rika kawo kudin ciyarwa na ’ya’yansa uku,” inji shi.